Harin Da Iran Takai A Sansanin Sojin Amurka A Kuwait Yayi Barna

harin iran yayi mummunar barna a hadaddiyar daular larabawa

Rahotanni sun bayyana cewa hare haren mayar da martani da dakarun sojin kasar iran suka yi da makamai masu linzami da jirage marasa matuki  a sansanin sojin Amurka a kasashen Kuwait da hadaddiyar daular larabawa ya lalata tsarin sadarwa da rumbunan ajiyar makaman yaki da kuma wuraren da sojoji ke aiki da kuma tsarin rada

Dakarun sojin sun ce an kaddamar da harin ne da sanyi safiyar ranar Alhamis  a matsayin ramuwar gayya ga shahadar fararen hula da sojojin iran a lokacin hare-haren amurka ba tare da laifin komai ba. yace makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki sun dira a filin saukar jiragen sama na Ahmed al-jabir na kasar Kuwait

Haka zalika sun bayyana cewa dakarun sun kaddamar da hari a kan sansanin amurka dake Minhab a hadaddiyar daular larabawa da jirage marasa matuki  da makami masu linzami, kuma ya lalata naurorin rada dake wajen. Wannan sanarwa ta zo ne bayan sabbin hare- haren da Amurka ta kai a kudancin kasar iran wanda kamar yadda ma’aikatar lafiya ta kasar iran ta sanar yayi sanadiyar mutuwar mutane 18 tare da jikkata wasu guda 142, daga cikin harin akwai wanda ta kai kan wajen bikin aure a garin Kouhestak a lardin Hormuzgon

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted