Ministan yaki na HKI Israel Kantz ya bayyana cewa gwamnatin HKI zata kori falasdinawa daga Gaza ta ta waye hanya hakan zai yi.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Katz yana fadar haka a wani taro wanda kafar yada labarai ta Ynet da kuma Jaridar Yedioth Ahronoth suka shirya a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa korar falasdinawa daga Gaza ya zama ita fi mafita tilo da ta ragewa yahudawan na gwace iko da Gaza, da kuma magance al-amarin gaza har abada.
Ya ce babu wata hanya ta magance batun samuwar Falasdinawa sai hijiransu daga Gaza ta sama, ta kasa da ruwa, duk wannan ba matsala ba. A halin yanzu inji Israel Katz ministan yakin HKI shi ne, amincewar shugaban kasar Amurka da kuma gamsar da kasashen da zasu karbi bakwancin falasdinawan.
Daga karshe ministan yakin ya ce, kasha 80% na Falasdinawa suna son ficewa zuwa inda zasu rayuwa da mutunci a ko ina za su sami haka a duniya.