16-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, wanda ni tahir amin nake kawo maku sau guda a ko wani mako. Da fatan zaku kasance tare da mu.
///..Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi maganar tarjama a zamanin Sarki Haruna Rasheed da dansa Mamon Abbasi. Daga ciki mun yi maganar Khawarizmi, malamin da yayi ficce a ilmin lissafi, ya kuma gano wasu fannonin ilmin lissafi wadanda suka hada da Logarism, da kuma wani mai suna Muthallath.
A cikin wannan fannin ilmin lissafi da ya gano, ana amfani da su a bangarorin kere keren zamani da dama. Mun kuma bayyana cewa, daga zamaninsu ne aikin tarjama ya fara sanyi a cikin daular musulunci, wannan kuma ba don kome ba sai don an daina gabatarda wasu sabbin ilmin da yakamata a yi bincike a cikinsu.
Wannan duk da cewa akwai sauran littafan da yakamata a ji yarjamarsu. Amma mafi yawan masu amfani da su an yi tarjamarsu, har an yi masu sharhi da karin bayani. A wasu fannonin ilmin malamai a cikin musulmi sun wallafa littafai sun rubuta sabbin ra’ayoyinsu ko ci gaban da suka gano a cikin fannonin da suka kore a kansu.
Wadannan fannoni daga baya an tarjamasu zuwa harsunan turanci don amfanin turawan.
A cikin wasu fannonin ilmi wadanda aka tarjamasu tun farko farkon tarjama, an yi masu sharhi an kara bincike a cikin fannin an rubuta wasu sabbin al-amura da aka gano, har ya zamu su wannan fannoni wadanda aka sami ci gaba a cikinsu an fara tarjamasu zuwa wasu harsuna.
Da haka kuma aikin tarjama ya fara rauni har ya kai ana tarjama ilmi daga harshen larabci zuwa wasu harsuna. Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa an fara tarjamar ilmi daga harshen larabci zuwa sauran harsuna tun karni na 3 hijira kamariyya.
Daga karshe a zamanin Yan gidan Buwaih, ko Alee Buwaih a cikin karni na 4 kamariyya aka kawo karshen tarjamar ilmi daga harsunan manya manyan kasashen da suka ci gaba a ilmi a lokacin zuwa harshen larabaci.
Sannan hakan ya faru ne a dai dai lokacinda daular musulmi ta rabu zawa kananan dauloli har hudu, a wancan zamanin. Sai ya zama tarjamar ta zama sai wadanda suke bukata ne a cikin daulolin musulunci suka ci gaba da tarjama.
Sai dai duk tare da cewa daular musulunci ta rarraba, amma a inda duk suke da manufa da amfani a haduwarsu suna haduwa, amma ko wace daula tana da irin nau’in shugabancinta.
A zamanin cibiyar ilmi ta tashi daga bagdaza ta wasu zuwa sabbin cibiyoyin daulolin da suka balle. Don haka su ma suka samar da cibiyoyin ilminsu. Don haka a wani bangare muna iya cewa cibiyoyin bincike da yada ilmi a cikin musulmi sun kara yawa, maimakon a da birnin Bagdaza kadai a yanzun ya yada zuwa wasu yankuna.
Bayan haka a yau zamu fara dubi dangane da wasi cibiyoyin ilmi a cikin daular musulunci bayan irin ci gaban da aka samu a karnoni masu yawa.
Banda ciyar Darul Hikma ko baitul Hikima, zamu ga cewa, wurare kamar masallatai da makarantu daban daban da dakunan ajiyar Littafai su ma sun zama wuraren yada ilmi da al-adu na addinin musulunci.
Shin yaya wadannan cibiyoyi suke aiki a lokacin? Wani tasiri suke da shi wajen gina fahinta da wayewar musulmi. ?
Mun san cewa amfani samar da wadannan cibiyoyi kamar makarantu da masallatai shi ne samar da musulmi na kwarai wanda ya fahinci addininsa ya kuma zama mai amfani da kawo ci gaba na al-ummarsa.
A cikin tarihi da kuma ci gaban addinin musulunci mun bayyana cewa masallaci shi ne cibiya na farko wacce take ilmantar da musulmi ya samar da wayewa gareshi ta yanda zai kasance musulmi na kwarai.
Manzon All..(s), a cikin masallaci na farko a Madina ne yake isar da sakon musulunci ga musulmi ya kuma umumin musulmi zuwa ga ayyukan alkhairi da kuma zama masulmi masu tsoron All..T,
Kamar yanda muka ambata a baya, masallaci na farko a musulunci, shi ne cibiyar bautar All..kuma makaranta, wurin tarbiya, da isar da sakonnin All..ga musulmi. Kuma daga nan ne manzon All..(s) yake ake tattauna al-amuran siyasa ko shugabanci, da yaki da kuma horarra da sojoji da alkalanci da sauransu.
Bayan manzon All..(s), Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) ya ci gaba da wannan tsarin, don haka shi ma a lokacinda ya sami damar shugabantar Al-Ummar musulmi, a Kufa yakan samra da lokuta daban daban na zama a cikin masallacinsa a Kufa inda zai yanke hukunci tsakanin mutane, ya nunawa alkalansadabarbarun alkalanci, wadanda addinin musulunci ya amince da su, a wasun kuma ya yada ilmin sanin All..fara daga tauhidi da limamanci, da adalcin All..da fikihu da sauransu.
A yaki ma yakan koyawa musulmi ka’idojin yaki a musulunci. Akwai hukunce hukuncen addini da dama wadanda manzon All..(s) a rayuwarsa bai sami damar fadawa musulmi ba, amma ya sanar da Aliyu wadanan hukunce hukunce, don ya sanar da musulmi ko ya aiwatasu a cikinsu.
Babban misali shi ne, a zamanin manzon All..(s) ba’a taba yaki tsakanin musulmi ba, kuma hukunce hukuncen yaki a tsakanin musulmi da kuma tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba sun bambanta.
Dukkan khudbobinsa da wasikunsa da maganganunsa suna dauki da ilmi. Wanda har yau musulmi suna amfana da shi.
Misali daga cikin wasikunsa mai cike da ilmi shi ne, takardan da ya rubutawa muhammadan dan Abubakar walinsa a kasar Masar dangane da hukunce hukunce na sharia da alkalanci da sauransu.
Haka ma wasikar da kuma umurnin da ya bawa Malik Al-Ashatar dangane da yanda shuwagabanni zasu kasance. Wannan bayan da Mu’awiya ya kashe gwamnansa a kasar Masar Muhammad dan Abubakar. Ya mayeshi da Malik Al-Ashtar sannan ya bashi wannan wasikar zuwa kasar Masar, amma Mu’awiya suka kasha shi ma kafin ya isa gidan gwamnati a kasar ta Masar.
A cikin wasikar ya fara da yi masa bayani dangane da mutanen masar yana cewa “zaka je wajen mutane, wadanda imma dan uwanka a addinin ko kuma mai kama da kai a halitta…”.
Daga nan yana fadawa Ashar kan cewa mutanen Masar, ko dai musulmi ne dan uwanka, ko kuma kiristoci masu kama da kai a mutuntaka….”
Ya cikin wasika maitsawo ya fada masa yadda zai jagoranci mutanen kasar, ya fada masa tsarin tafiyar da mutanen daban daban. .. wanda yake son karin bayani ya nemi wannan wasika ko takardar Amirul muminina(a) ga Malikul Ashtar.
Don haka bayan shahadar Amirul muminina (a), dansa Imam Al-Hassan (a) ya ci gaba da wannan tafarkin na ilmantar da mutane a masallaci ko kuma a duk inda ya sami damar yin hakan.
Hakama wannan al-adar ta yadu a kasashen musulmi, inda masallatai da dakunan karatu, ko buyutul Hikima da makarantu suka zama wuraren karantarwa.
Wannan halin ya ci gaba har zuwa zamanin limamai na 6 daga limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All…(s).
A zamaninsa a kuma mazhabar iyalan gidan manzon All..(s), ya koyawa mabiyansa fannonin ilmi da dama. Ya kuma koyawa masu ilmin addini na gaskiya na gidan annabta.
Masali, Imam Assadik (a) ya koyawa Aban dan Taglab, ilmin fikihu na iyalan gidan manzon All..(s), ya kuma umurce shi da ya zauna a masallaci ya fada fatawa, ya koyawa mutane ilmin addinindu.
Sai kuma Hisham dan Hakam wanda ya kware a ilmin kalam, ko akidu da kuma jayayya a kan akidu a cikin musulmi ko wajensu. Ya umurce shi da ya zauna a cikin masallaci shi ma, ya tattauna da mutane matsalolin da suka shafi akida da addi nai.
Sannan Imam Assadik (a) yana da dalibi wanda ake kira Jabir dan Hayyan, wanda yak ware a fannonin ilmi daga ciki har da ilmin kimiyar sinadarai.
Hakama Imam Assadik (a) ya koyawa wasu ilmin gywaje gyaje, kuma ya koyawa wasu daga cikin dalibansa. Imam (a) ya na himmatuwa da ilmin gwaje gwaje da kuma na tunani. Don haka a jami’arsa da ke madina ya karantar da mutane kai tsaye ko ta dalibansa kimani 4, 000.
Shio ne ake ganin ya samar da mazahbar shi’a mai limamai 12, sai dai muna iya cewa shi ne yasami dama daga cikin limaman ya watsa ilmin iyalan gidan manzon All.l.(s).
Mafi yawan karantarwa Imam Assadik ya gabatar da su a masallaci ne, a madina ko a Kufa ko kuma wani wuri. Sannan dalibansa ba sun yada ilmin da suka samu ne a cikin masallatayya.
Don haka masallaci shi ne cibiyar yada addini na farko a musulunci. Sannan hatta bayan an samarda makarantu, masallatai sun ci gaba da kasancewa wurin ibada da kuma yada ilmin addini a musulunci.
Bayan samar da makarantu, masallaci ya ci gaba da zama cibiyar samar da tarbiyya da kuma daukan darussan halaye masu kyau ko Akhlaq. A matsayin misali, a yankin Sistan an gina masallaci a yankin a karni na farko bayan hijira. Wanda ya ci gaba da zama wurin koyon ilmin addini da na tarbiyya.
Hakama a Bukhara, sannan Nishabur ayankin Khurasan, an gina masallatai da dama. Saboda gari ne na harkokin siyasa da kuma ilmi. Don haka akwai masallatai da dama a garin, wadanda wasunsu har yanzun suna tsaye. Kamar masallacin Akilu da tsohon masallaci da sauransu. Ana bada ilmi ana kuma ci gaba da tarbiyan mutane a cikinsa.