Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 215

215-Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmi na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

215-Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmi na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (s) dan Faah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo mako, a cikin shirimmu da ya gabata mun fara Magana dangane da yadda Mu’awiya dan Abu sufyan ya sabawa dukkan al-kawulun da ya daukawa Imam AL-Hassan (a) kafin ya mika masa shugabancin Al-ummar musulmi.

Mun bayyana cewa, alkawali na farko wanda ya dauka daga wajen Ma’awiya shi ne kada ya zagi mahaifinsa Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib(a), amma a cikin khudubarsa ta farko, a masallacin Amirulmuminina (a) a Kufa,  Mu’awiya ya  kafa sunnar zagi da la’antar Amirul muminia (a) da kuma sauran iyalan gidan Manzon All..(s) masu tsarki. Wannan sunnar ta wanzu har zuwa shekaru kimani 60 a cikin al-ummar musulmi ko  fiye da haka.

Wannan halin ya ci gaba har zuwa zamanin sarki Umar dan Abdulazizi, sarki na 8 daga cikin sarakunan Banu umayya. Wanda ya kawo karshen zagin, sannan yam aye shi da wata ayar al-kur’ani mai girma wacce All…yake fada:

{Lalle Allah nã yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma’abũcin zumunta, kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama’a. Yanã yi muku gargaɗi, tsammãnin ku, kunã tunãwa.} Annahal 90.

Wannan kamar yanda muka fada, hakan ya faru a cikin musulmi na tsawon wannan lokacin duk tare da cewa akwai hadisan manzon All..(s) da dama, wadanda suka inganta kan cewa, zagin Aliyu zagin manzon All..(s), sannan zagin manzon All..(s) zagin All..don haka musulmi sun dau shekaru kimani 60 wasu sunce fiye da haka suna zagin manzon All..(s) a kan mimbarinsa a bayansa.

A wasu hadisan yana cewa {wanda ya cutar da Aliyu ya cutar da ni}, a wani hadisin yana cewa {Ya Ubangiji ka jibanci wanda ya jibance shi, ka tabar da wanda ya tabar da shi, ka riskar da gaskiya da shi ta duk inda ya kewaye.. } a wani hadisin yana cewa {Shin baka son (ya Aliyu) ka sance} matsayinka da ni, kamar matsayin haruna da musa ba? Sai dai babu annabi a baya na,}.

Da wannan muna iya cewa babu wani sahabin manzon All..(s) wanda aka zaga a bayan wafatinsa (a) kamar Aliyu dan Abitalib (a) da yayansa. Wadanda, matsayinsu ya fi matsayin sauran sahabban manzon All..(s). Su ne tsarkakakku ko Ahlul baitin manzon All..(s). Wasu malaman tarihin musulunci sun yi kokarin  boye falalarsu ta hanyar canza ma’anar Alhlul baiti.(a). da cewa Ahlulbait sune, Yayan Aliyu, da Jaafaru, da Akilu da Abbas.

Ko ta hanyar kirkiro hadisai su jinginawa manzon All..(s) wadanda zasu batarta matsayinsu.  Amma duk da haka sai da gaskiya ta bayyana.

Da farko aya ta 33 cikin surar Ahmzab, bangare na karshe na ayar yana da bambanci da farkon ayar.tunda bangare na farko yana maganar matan manzon All..(s) ne, amma karshensa sai All..ya canza lamirin wadanda ake Magana akansu daga mata su kadai, zuwa jam’in maza da mata.

Na biyu ayar tana maganar tsarki irin ta zuciya ne ba na dauda ko zahiri ba, sannan a cikin matan manzon All..(s) ba wacce ta taba fadar cewa tana tsarki daga zunubi, wasu daga cikinsu sun shidawa Fadima(a) diyarsa tana da tsarki daga zunubi. Ita ma (s) ta yi ikrarin tana da tsarki, don haka ina maganar cewa, ayar tsarki ta 33.33 tana nufin matan sa ne (s)?

Banda haka wasu ayoyin al-kur’ani mai girma sun fito a fili suna tabbatar da cewa wasu daga cikinsu sun aikata laifu.

Wasu ayoyin kuma sun bayyana matsayin da girman da matan manzon All..(s) suke da shi a wajen All.., amma da sharudda, na tsorin All..(T). Wanda ya tabbatar da cewa suna iya yin sabon All…sannan ta kara da cewa idan wata daga cikinsu ta kuskura tayi sabon All..All..zai ninka mata azaba a ranar kiyama, wacce ta kyautata kuma zai ninka mata lada saboda darajar mijinta manzon All…(s).   kamar yanda wannan ma’anar ta bayyana a cikin aya ta 32 na suratul Ahzab.

Banda haka, ba wanda ya taba cewa shi ma’asumi ne, baya kuskure a cikin al-ummar musulmi musamman sahabban manzon All..(s) sai Ahlul baiti(a), kuma sune Aliyu, da Fatimah matarsa kuma diyar manzon All..(s) da kuma yaynsu Al-Hassan da Alhussain(a) tare da yayan Alhusain 9, a wasu hadisan.

Ko wanne daga cikinsu yana ikrarin cewa shi baya kuskure, kuma shugabancin al-ummar musulmi bayan manzon All..(s) nasu ne.

Banda haka, hadisai ingantattu sun tabbata daga manzon All..(s) yana cewa { Aliyu dan uwansa ne, wasiyinsa ne, kofar ilminsa ne, harunana ne, Khalifana ne, ba don kariyarsa ba da addinin musulunci bai tsayu ba, , da ba wanda zai bautawa All..da addinin musulunci, da ba wanda ya kadaita All…….da sauransu}.

Wani ya tsara kasida dangane da Aliyu (a) yana cewa:

Shin a kan mimbarori ne kuke daukaka murya da zaginsa? Alhali da takobinsa ne aka kafa muku ginshikan addinin?.

Amma dalilin da mu’awiya ya dage a kan zaginsa shi ne, kamar yanda ya sha nanatawa da kansa yana cewa, ‘idan bai kaskanta Aliyu (a) a gaban jama’a ba, ban isa shugabantar mutane ba.’.  

Malaman tarihi sun bayyana cewa a lokacinda Imam Al-Hassan(a) ya mikawa Mu’awiya shugabancin al-ummar musulmi, ya koma sham sai ya tara mutane yayi masu khuduba, a cikin khudubarsa yana cewa: Ya ku mutane, lallei manzon All..(s) ya ce mani, Lalle kai zaka sami khalifanci a baya na, (idan haka ya  faru) to ka zabi kasa mai tsarki, (yana nufin sham, inda masallacin Kudus yake)  don akwai Abdalu a cikinta, hakika na zabe ku, ku la’ani baban turbaya..(wato Aliyu(a)).

Sai mutane suka fara la’antarsa suna aibata shi. Daga nan Mu’awiya ya maida la’anarsa sunna a duk lokacinda yayi khuduba a ranar Jumma’a ko idoji,  a karshensu  sai ya la’ani Aliyu dan Abitalib (a).

Ga kuma yanda sunnansa ta la’anar take, idan ya yi khuduba ya kare sai ya cewa: Ya Ubangiji ! Lalle baban turbaya ya aikata kafirci a cikin addininka, ya toshe tafarkinka, ka la’anceshi la’ana mai yawa, ka kuma azabtar da shi azaba mai radadi.

Wadannan kalmomi ne yake fada a kan mimbari, sannan bayan al-amura suka tabbata a gareshi, sai ya rubutawa ma’aikatansa a sauran garuruwa tare da umurnin su la’ani dan uwan manzon All..(s) kuma shugaban wannan al-ummar (a) a bayansa a cikin  kudubobinsu.

Don haka wakilansa a dukkan kasashen musulmi hatta a madinan manzon All..(s) kusa da kabarinsa(s) suna daga murya suna la’antar Aliyu(a) a kan mimbarin manzon All..(s). Sunan la’antarsa suna barranta kansu daga gareshi(a).

Amma a cikin wannan halin, menene matsayin Amirul muminina (a) a zagin da Mu’awiya yake masa, don ya fara zaginsa tun yana da rai, tun bayan yakin siffin. Haka ma menen matsayin dansa Imam Al-Hassan (a) kan zagin da Mu’awiya yake wa mahaifinsa (a)?.

An ruwaito cewa, Imam Ali (a) ya ji wasu daga cikin sahabbansa suna zagin Mutanen sham a dai dai lokacinda ake yaki a siffin, sai ya ce masu: {Ni bana son ku kasance masu zage-zage, sai dai, da kun kun sifanta ayyukansu, kuna kuma ambaton halayensu, da yafi zama dai dai a zance, da kuma ya fi zama sauki a sauke uzuri.

Da kun fada, maimakon zaginsu, kuna cewa: Ya ubangiji ! ka tsare jinanemmu da jinanensu, ka kyautata a tsakanimmu, ka shiryatar da su daga batan da suke ciki, don su gane gaskiya, daga batan, su kaucewa bata, da tsokana..} wannan shi ne matsayin Imam Ali (a) dangane da mutanen sham daga ciki har da Mu’awiya dan Abusufyan. Wannan kamar yadda ya zo a cikin sharhin Nahjul Balaga na Ibn abil Hadid, JZ na daya. SH 420.

Sannan haka ma dansa Imam Al-Hassan (a), kamar yadda shi ma, an ruwaito cewa: Wani manzon Mu’awiya ya zo masa daga sham, sai ya ga Haibar Imam Alhassan (a) ya kuma kayatar da shi, sai yace masa, ‘Ina rokon All..ya kiyayeka ya kuma halaka wadannan mutane’.

Sai Imam Al-Hassan (a) ya hana shi fadar haka,  ya ce masa {Kayi a hankali wannan mutum, kada ka kha’inci wanda ya amince da kai, ya iceka ka so ni don manzon All..(s) da babana da mahaifiyata. Kha’inci ne mutane su amince da kai, sai kai kuma kana adawa da su} Almalaahim Walfitan 143.

Wannan shi ne, matsayin Imam Ali (a) da kuma dansa Imam Al-hasan(a) dangane da Mu’awiya da mutanen Sham. Matsayinda, idan ba su ba, da wuya ka sami mai yin haka.

Bayan da Mu’awiya ya sunnata zaginsu a kan mimbarorin musulmi a dimash, Mu’awiya bai tsaya nan ba, sai ya rubuta takarda guda,  ta biyu, ga ma’aikatansa inda yake cewa:

‘Ni na kubuta daga duk wani daga cikinsu wanda ya ruwaito hadisi dangane da falalar Abuturab da iyalan gidansa.’

Subhanalla ! Don haka ma’aikatan nasa gaba daya suka haw kan mimbarori suka fadawa musulmi kada wani ya ruwaito hadisi daga manzon All..(s) wanda yake magana a kan falalar Aliyu dan Abitalib (a) ko kuma iyalan gidansa, su waye iyalan gidan manzon All..(s)? sune Aliyu da matarsa Fatima da alhassan da Alhussain (a).

Mu’awiya ya san cewa babu wani musulmi wanda yake da falala da matsayi a wajen All..da manzonsa (s) kamar wadan nan. Don haka yana son ya hana wadannan falalolin su yadu a cikin bayin All…

Sai dai wannan mani mataki ne wanda ya kammala shirin da Khalifofi na farko suka yi na hana yada hadisan manzon All..(s) a cikin musulmi, saboda me daruruwan ayoyin Alkur’ani mai girma sun sauka dangane da falalolinsu da kuma girmansu,  wadannan musulmi ba zasu sani ba sai tare da wadannan hadisan.

Don haka hana ruwaito hadisan manzon All.., ya nuna ba’a son sanin hakikanin fassarar wadan nan ayoyin daga bakin manzon All..(s) ne. Don haka suna da damar fassara ayoyin ta yanda suka ga dama. Kamar yanda suka yiwa aya ta 33.33.

Don haka Mu\awiya ya fito fili ya bayyanawa musulmi kan cewa, saboda hana yaduwar falalar wadan nan iyalan gidan manzon All..ne aka hana ruwaito hadisai, don haka ba’a son a ji hadisan falalar Aliyu dan Abitalib(a) ne da iyalan gidansa.

Don haka haramun ne a cikin al-ummar musulmi a lokacin wani ya ruwaito hadisa wanda yake maganar cewa Aliyu dan abitalib (a) ko yayansa Alhassan da Alhussain da kuma mahaifiyarsu diyar manzon All..(s) suna da wata falala. Inna lillah wa inna ilaihi raji’un,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted