Jamus Ta Ta Sayarwa HKI Makamai Na Dalar Amurka Miliyon $930

Gwamnatin kasar Jamus ta amince da sayarwa HKI makamai wadanda zata ci gaba da amfani da su don kissan Falasdinawa a Gaza, wadanda kimarsu ya

Gwamnatin kasar Jamus ta amince da sayarwa HKI makamai wadanda zata ci gaba da amfani da su don kissan Falasdinawa a Gaza, wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka miliyin $930.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar Der Spiesge wacce ta bada wannan labarin a jiya Laraba, ta kara da cewa,

Berlin ta amince da sayarwa HKI wadannan makamai a tsakanin watan Jeneru na wannan shekara ta 2026 zuwa watan Yuni kawai.

Wato watanni 6 na farko, amma a wannan shekarar gwamnatin Chancellor Friedrich Merz ta sayarwa HKI makamai wadanda suka ninka na shekara ta 2025 har sau 4.

Labarin ya kara da cewa 1/5 na makaman sun fito ne daga yarjeniyar makamai tsakanin Jamus da HKI ne.

Sannan 1/3 daga cikinsu sun shafi kamfanin INS Drakon wanda ya gina makaman submerin mai suna ‘ Dolphin II-class submarine ‘. Jirgin ruwa na karkashin ruwa wanda tsawonsa ya kai mita 70. Kuma an kammala aikin a halin yanzu yana kan hanyarsa ta zuwa HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted