Denmark Ta Aike Da Sojojinta Zuwa Yankin Greenland

kasar denmark na kara tabbatar tsaro a yankin green land don tunkarar Amurka

Rahotannni sun bayyana cewa kasar Denmark ta aike da dakarun sojinta zuwa yankin Greenland a wani bangare na kara karfinta wajen tunkarar matakin da Amurka take son dauka na amfani da karfin soji wajen kwace yankin baki daya

Copenhagen ta aike da tawagar farko na dakarunta zuwa yankin Greenland a wani mataki na kara fadada mataken soji a yankin , a wani shiri da kasar Denmark ke yi na kara bunkasa karfin sojinta a yankin.

Wannan mataki yana daya daga cikin tsarin kungiyar tsaro ta Nato ta kaddamar a wannan shekara na kara karfinta a yankin, tare da kawayenta sakamakon barazana da shugaban Amurka Doland trump ke yi na neman tada zaune tsaye .

Cofenhegen ta yi alkwarin ba da biliyoyin daloli don kara karfafa tsaro  bayan ministan tsaron kasar ta Denmark  Troels lund poulse yayi alwashin zuba hannun jari mai yawa na tsawon shekaru a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted