HKI : Zasu Kori Falasdinawa Daga Gaza Ta Kowanne Hali

shirye-shiyen da isra'ila ke yi na korar falasdinawa daga gaza da goyon bayan Amurka

Ministan kula da harkokin soji na HKI Israel Ketz ya bayyana cewa gwamnatin sahyuniya za ta kori  falasdinawa daga yankin falasdinu ko ta halin kaka madama shugaban Amurka Donald Trump ya bada dukkan goyon bayan da ake bukata a kan shirin,

Da yake Magana a wani taron da Israel news ta shirya a jiya laraba  Isreal katz yayi ikirarin cewa ci gaba da kai hare hare a yankin gaza shi ne mafita ga manufar da muke son mu cimmawa, yace babu mafita ga yankin gaza ba tare da gudun hijira ba, yace abin da tel aviv take shiryawa shi ne ganin ta kori falasdinawa daga yankin gaza baki daya ta kowanne hali

Haka zalika ya bayyana cewa Trump ya amince zai yi kokari wajen ganin ya gamasar da sauran kasashe su amince da falasdinawa yan gudun hijra , sai dai abin da ya kawo jinkiri shi ne yadda sauran kasashen za su amince da bukatar amurka ,

Isra’ila ta kaddamar da yakin kare dangi kan alummar gaza a ranar 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 bayan da kungiyar hamas ta kaddamar da harin dufan aqsa a matsayin martani kan hare -haren wuce gona da ira da hki ke yi kan alummar falasdinu, sai dai bayan shekaru biyu isra’ila ta amince da tsagaita wuta bayan kasa cimma burinta na shafe kungiyar Hamas da kwato yahudawan dake hannun Hamas

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted