216-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kansance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma sirar Imam Al-Hassan Almujtaba (a) dan Fatimah(s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, mun tsaya inda muka fara kawo muku yanda Mu’awiya dan Abusufyan ya sabawa al-kawulan da ya daukawa Imam Al-Hassan (a) kafin ya mika masa shugabancin Al-ummar musulmi.
Daga cikinsu mun yi maganar zagin Amirulmuminina (a) da iyalan gidan manzon All..(s) a kan mimbarorin musulmi. Da farko Mu’awiya yace manzon All..(s) ya bashi busharar zai sami shugabanci, sannan ya ce masa, ya zami sham, don akwai Abdalu a cikinta. Sannan ya ce ya zabi mutanen sham, daga karshe ya ce masu su zagi Abu turab wato Imam Ali (a).
Sannan ya rubuta wasika guda wa ma’aikatansa, ya su la’ani abuturab da iyalan gidansa a duk khudubar da suka yi, a jumma’a da kuma idoji biyu. Don haka dubban limamai a cikin al-ummar musulmi sun dauki wannan umurnin sun kuma maida zagin Imam Aliyu dan Abitalib (a), da iyalan gidansa sunna, har zuwa shekara ta 99 bayan hijira a lokacinda Umar dan Abdul-aziz ya hau kan kujerar sarauta na banu umayya.
Mun bayyana cewa a cikin khudubarsa ta farko bayan da Imam Al-hassan (a) ya mika masa shugabancin Al-ummar musulmi a masallacin kufa, sai ya fara da la’antar Amirul muminina Aliyu dan Abu talib (a), sai da Imam Al-Hassan (a) ya tashi ya mayar masa da martani.
Mu’awiya da ma’aikatansa sun maida la’antar Aliyu dan Abitalib da Iyalan gidansa (a) bangare na khudubar Jumma’a da kuma sauran idoji biyu. Kuma duk wanda ya ki yin haka yakan tube shi daga aikinsa. Kamar yanda ya tubi Sa’id dan Assi a matsayin walinsa a Madina a lokacinda ya ki la’antar Imam a kan mimbarin manzon All..(s) a Madina. Ya mayeshi da Marwan dan Hakam wanda ya ci gaba da hakan.
Marwan dan hakam yaci gaba da la’antar Imamu Ali (a) kan mimbarin manzon All..(s) har sai ya kai ga Imam Al-Hassan (a) wanda yake rayuwa a cikin madina a lokacin ya daina zuwa masallaci don sallar Jumma’a.
Malaman tarihi sun bayyana cewa Mughira dan Shuba ya yawaita la’antar Amirulmuminina (a) a kan mimbari har ya manta yawan za’ginsa da yayi, don yawansa.
Sannan Zaiyad dan Sumayya yana kwadaitar da mutanen kan hakan, wanda yaki yakan kawo takobi ya katse wuyarsa.
Al-amarin ya kai ga dayansu idan ya manta da la’anta a cikin khuduba, sai yayiu kala’insa a tafiya. Sai suka gina masallaci a wurin suka sanya masa suna ‘masjidu Azzukir’.
An nakalto cewa, Hisham dan Abdul Malik dan Marwan yayi khudba a Arafa, sai bai yi la’ana ba, Sai Abdulmalik dan Walidu ya ce masa bai yi dai dai ba. Ya ce masa ‘Ya amirul muminina wannan rana ce wacce khalifofi suke son a la’antar Abuturab. Sai Hasham y ace masa ‘ba don wannan muka zo ba’.
A lokacinda Abdulmalik Dan Marwan ya zama Khalifa ya himmatu da La’antar Imam Ali (a). Ya kuma game dukkan al-ummar musulmi wajen aikata haka. Kuma an ruwaitoshi yana fajirci da yin haka a fadarsa.
Sannan Khalidu dan Abdullahi Alqasri, wanda ya kasance ma’aikacin sarakunan banu Umayya a Makka da kuma Araqi daga baya, yana bayyana la’anar Amirul Muminina Aliyu dan Abitalib (a) a fili.
Idan yah au kan mimbari ya kuma yi Khuduba idan ya zu wajen la’ana sai yayi ta tsallae, yana cewa “Ya Ubangiji la’ani Aliyu dan Abitalib dan Abdul muttalib surukin manzon All..(s) a kan diyarsa, kuma baban Al-Hassan da Hussaini.’.
Idan ya yi haka sai ya juya kan mutane ya ce masu: Na saka ya sunan ne? .
Dangane da Khalidu dan Abdullahi Alqasra, malaman tarihi sun bayyana cewa, mahaifiyarsa kirista ce, don haka ya gina mata cocu tana bauta a cikinsa.
Kuma dangane da haka ne, Farazdak ya tsara wata kasida yana aibata shi a cikinta.
Hafiz Suyudi, yana cewa, a zamanin banu umayya ana da masallatan Jumma’a fiye da 70,000 wadanda ake zagin Amirul muminina (a) a cikinsu. Wannan yana daga cikin sunnar Mu’awiya dan Abusufyan.
Malaman tarihi sun bayyana cewa, a lokacinda zajin Amirulmumina (a) a sami karbuwa a cikin mafi yawan mutane wawaye, wadanda basu san matsayinsa ba. Sai wasunsu suka maida zagin wata hanyar samun kusanci ga sarakuna da kuma ma’aikatansu.
An ruwaito cewa, daya daga cikin wawayen, ya je gaban Hajjaju dan Yusuf Athaqafi, ya daga muryarsa yana cewa (Ya kai Hakimi, lallai iyayen na sun cutar da ni, da suka sanya masani suna Aliyu, lai ni mabuka ci ne fakiri, wanda yake bukatar kyautarka) sai Hajjaju ya ji dadi ya yi murmushi, sai ya ce masa: Saboda tawsayin wand aka kama kafa da shi jeka na baka shugaban cin kaza.
Malaman tarihi sun bayya cewa, zagi da la’antar Amirulmumina (a) ya yadu a cikin dukkan kasashen musulmi sai Sijistan, inda sau guda ne kawai aka la’ane shi a kan mimbarinshi.
Mutanen yankin sun ki amincewa a la’aneshi a kan mimbarorinsu, a lokacinda Umayyawa sun ga cewa sun dage kan matsayinsu sai suka amince masa su yi khudubobinsu ba tare da zagi ba.
Don haka mutanen Sijistan sun sami wannan daukakar, kuma sun kafa tarihi kan wannan matsayin da suka dauka, kin amincewa a zagi waliyin All..a kan mimbarin musulmi.
Wannan halin ya ci gaba a cikin daular umayyawa, har zuwa lokacinda Umar dan Abdul aziz ya sami sarauta. Ya haramta zagin ya kuma rubutawa ma’aikatansa a ko ina a cikin daular musulunci su daina zagin. Ya bada umurni da su musanya zagin da suke yi a cikin khudubobinsu na Jumma’a da kuma Iduna wannan ayar inda All…T yana cewa
{Ya Uabngiji ka gafarta mana, da kuma yanuwammu wadanda suka rika mu Imani, kada ka sanya kunshi a cikin zukatammu ga wadanda suka yi Imani, Ya Ubangijimmu lalle kai man jinkai ne da tausayi} Suratul Hashr Aya ta 10.
Ko kuma wasu suka ce, ya umurcesu su maye kalmomin zagi da aya wacce All..T yake cewa
{Lalle All..yana umurni da adalci, dakyautatawa, da kyauta ga ma’abuta kusanci, kuma yana hana alfasha da munkari, da kuma tsokana, yana muka gargadi mai yuwa ko yi tunani} Annahal 90. Wasu kuma suka ce ya hada ayoyin guda biyu, ya ce a karantasu a maimakon zagin da la’anar Amirulmuminina Ali(a).
Tare da wannan ya kafa tarihi wajen kawo karshen wannan musibar ta zagin manzon All..(s) a kan dubban mimbarorin musulmi tare da zagi ko la’anar Imam Ali (a) a kansu.
Ya kafa tarihi, wanda ba za’a taba manta da shi a tsawon tarihin bil’adama. Ibn Abil Hadid mai sharhin Nahjul Balagha ya nakalto cewa, dalilanda suka sa Umar dan Abdul azizi ya hana zagi da kuma la’antar Amirulmumina (a) kan mimbarorin musulmi sun hada da cewa
Wata rana yana yaro karami yana kuma karatun Alkur’ani a gaban wani malami daga cikin yan gidan Utbanu dan Masud. Sai wata rana ya zo zamu yi karatu, sai ya ganni ina wasa sannan a cikin wasammu yana la’antar Aliyu dan Abitalib (a), daga baya sai na bar wasan na je wajensa don mu yi karatu, sai ya shiga masallaci ya fara sallah (nafila) ya tsawaita sallah, ni kuma ina jiransa.
Sallar ta sa ta yi tsawo har na fahinci cewa da gangan yayi don baya son karantar da ni. Amman a ci gaba da jiransa har ya sallame. A lokacinda ya sallame sai yayi mani wani irin kallo a fuskanta, sai na ce, masa ya Sheikh yau lafiya kuwa?
Sai yace mani, a yau kana zagin Aliyu dan Abitalib(a), ? sai na ce , EE?
Sai ya ce mani, Way a fada maka All.. ya yi fushi da ma’abuta yakin Badr bayan ya yarda da su?.
Sai nace: Ya baba na shin Aliyu yana daga cikin wadanda suka halarci yakin Badar ne? sai yace: Kaitinka ! Shin yakin badar yana da wani wanda ba Aliyu ba? . sai nace masa b azan sake ba.
02-Sai kuma na kasance ina sauraron mahaifina sarki Abdul aziz yana khuduba a kan membari, ina fahintar irin fasahar da yake da ita a khudubarsa, amma sai na fahinci cewa, a duk lokacinda yazo gabar la’ana a karshen khudubarsa, sai muryarsa ta canza tana rawa kamar wanda bai iya magana ba. Sai wata rana na tambaye shi, na ce masa ya babana ni na lura da wani abu danagne da kai inda kana Khuduba, kana magana da fasaha da hikima, amma idan kazoo kan zagin wannan mutum yana nufin (Imam Ali(a)) sai ka zama kamar wanda baya iya magana, me yasa haka yake faruwa?.
Sai sarki Sarki Abdul Aziz ya ce masa, ai idan da mutanen da suke karkashin membarorimmu zasu san matsayin wannan mutum (yana nufin Aliyu dan Abitalib(a) da ba zamu iya mulkansu ba.