Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta neman ta kara tada zaune tsaye a yankin
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Iran ba ta neman fadada yanayin tashin hankali da rashin tsaro a yankin.
Shugaban ya jaddada cewa: Iran ba ta neman fadada yanayin tashin hankali da rashin tsaro a yankin, amma za ta yi duk abin da za ta iya don kare tsaronta, muradun kasa, da kuma cikakken ikon yankinta.
Pezeshkian ya bayyana a jiya Litinin, 12 ga watan Agusta cewa: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta son kara tada rikici ko kawo cikas ga tsaro a yankin, amma za ta kare tsaronta, muradun kasa, da kuma cikakken ikon yankinta da dukkan karfinta.”
Ya kara da cewa: “A lokaci guda, karfafa jarin zamantakewa, inganta lafiyar jama’a, da kuma kara juriyar kasa suna daga cikin muhimman ginshikan karfin kasar.”