Pezeshkian: Fadada hulda tsakanin Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa maslaha ce ga musulmi

Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya jaddada bukatar fadada huldar dake tsakanin Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa domin amfanin kasashen biyu da kuma al’ummar musulmi,

Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya jaddada bukatar fadada huldar dake tsakanin Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa domin amfanin kasashen biyu da kuma al’ummar musulmi, tare da fatan ganin alaka da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu za ta kara fadada a nan gaba.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya habarta cewa, Dr. Masoud Al-Badzikian a yammacin ranar Talata 30 ga watan Yuli, ya bayyana fatansa a ganawar da Sheikh Abdullah bin Zayed mataimakin firaministan kasar UAE kuma ministan harkokin wajen kasar,  wanda ya isa birnin Tehran domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar ta Iran.

Yayin da yake bayyana cewa zurfafa da karfafa alaka da kasashen da ke makwabtaka da Iran, yana daga cikin manyan abubuwa masu fifiko a cikin manufofin siyasar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Shugaban ya ce: Kasashe da al’ummomin musulmi ‘yan uwan ​​juna ne, kuma idan suka hada kai to gwamnatin sahyoniya  ba za ta iya aikata irin wadannan munanan laifuka akan al’ummar Palastinu ba.

Pezeshkian ya bayyana fatan cewa fadada huldar da ke tsakanin kasashen biyu za ta haifar da hadin kai da hadin gwiwa tsakanin kasashen musulmi.

Sheikh Abdullah bin Zayed mataimakin firaministan kasar  kuma ministan harkokin wajen kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, ya taya shugaban kasar Iran murnar zabensa da kuma rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, yana mai cewa: Gwamnati da al’ummar UAE na da imanin cewa, karfafa alaka tsakanin kasar da kuma Iran, zai samar da damammaki masu yawa ta yadda al’ummomin kasashen biyu za su amfana da juna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments