Jam Kamal Khan ministan kasuwanci na kasar Pakisatan ya bayyana cewa ziyarar da shugaba Pezeshkiyan na kasar Iran ya kawo Islam’abad yayi armashi, kuma ya bude wasu hanyoyi da dama harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Khan ya kara da cewa a yau al-ummar musulmi suna alfakhari da JMI sabado nasarar da ta samu kan HKI, kuma suna ganon hakan a matsayin abin girmamawa ga kasar da kuma sauran kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday ta nakalto daga IRNA wanda yake cewa ministan kasuwanci na kasar Pakisatan da kuma ministan ma’adinai masana’antu da kuma kasuwanci na kasashen biyu sun gana a rana ta biyu da ziyarar shugaban zuwa Islamabad.
A tattaunawa ministocin Khan da kuma Mohammad Atabak kasashen biyu sun amince su bude kasuwar da babu kudaden fito a kan iyakokin kasashen biyu.
Daga karsheJam kamal Khan ya taya mutane da gwamnatin kasar Iran a kan nasarar da suka samu kan HKI a yakin kwanaki 12 a cikin watan Yulin da ya gabat.