Search
Close this search box.

OIC : Kisan Hanineh Keta Hurimin Kasar Iran Ne

Kungiyar Hadin Kan Musulunci ta ce Isra’ila ce, ke da alhakin” kashe shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas ta Falasdinu, Ismaïl Haniyeh, a makon jiya

Kungiyar Hadin Kan Musulunci ta ce Isra’ila ce, ke da alhakin” kashe shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas ta Falasdinu, Ismaïl Haniyeh, a makon jiya a Tehran.

A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan wani taro na musamman a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, kungiyar OIC ta ce “tana rike da Isra’ila, da cikakken alhakin wannan danyen harin”, wanda kuma ta bayyana a matsayin “keta hurumin kasar Iran.

Mambobin kungiyar 57 sun fitar da sanarwar ne jiya Laraba a karshen wani taronsu na musamman da aka gudanar a birnin Jeddah bisa bukatar Jamhuriyar Musulunci da Falasdinu.

OIC, Ta ce “gwamnatin mamaya ita ce ke da “cikakken alhakin wannan mummunan harin” wanda ya hallaka shugaban ofishin siyasa na gwagwarmayar Falasdinawa da kuma daya daga cikin masu tsaronsa a Tehran.

Hukumar ta kara da cewa, wannan danyen aikin ya zama wani laifi na wuce gona da iri, da kuma keta dokokin kasa da kasa da na Majalisar Dinkin Duniya.

OIC, ta yi gargadin cewa laifuffukan da gwamnatin ke ci gaba da yi, na kawo cikas ga tsaro da zaman lafiya a yankin, tare da yin kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya shiga tsakani cikin gaggawa.

Saudiyya ta yi wannan tsokaci ne, wanda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Waleed al-Khereiji ya ce kisan Haniyeh ya kasance “cin zarafi ne” na Iran.

Jim kadan kafin hakan, Saudiyya ta bayyana wannan kisa a matsayin keta hurumin kasa da kasa da kuma tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments