Nijar Ta Mika Ta’aziyyarta Ga Iran, Game Da Rasuwar Ra’isi 

Shugaban Majalisar Tsaron kasa ta Nijar, Birgediya Janar Abdourrahmane Tiani ya gabatar, ya jajantawa gwamnati da kuma al’ummar Iran bayan rasuwar shugaba Ebrahim Ra’isi. Bismillahir

Shugaban Majalisar Tsaron kasa ta Nijar, Birgediya Janar Abdourrahmane Tiani ya gabatar, ya jajantawa gwamnati da kuma al’ummar Iran bayan rasuwar shugaba Ebrahim Ra’isi.

Bismillahir Rahmanir Rahim lnna Lillahi wa lnna alayhi Rajiou’n

“A cikin bakin ciki da kaduwa ne na samu labarin a ranar 19 ga Mayu, 2024, na Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, mai girma Ebrahim Ra’isi a wani mummunan hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu, tare da wasu mukarabansa, in ji shugaban na Nijar a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litini. 

 “A cikin wannan yanayi mai radadi, da sunan majalisar ceton kasa da Gwamnati da al’ummar Nijar muna nuna bakin ciki da kuma gabatar da ta’aziyyarmu. 

”Muna kuma mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.”

“Al’ummar Nijar, wadanda labarin wannan bala’in ya girgiza su, suna nuna bakin ciki tare da tabbatar muku da hadin kai a wannan mawuyacin hali” a cewar sanarwar.

”Muna kuma fatan Allah ya jikan Ra’isi da dukkan wadanda lamarin ya shafa”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments