Jamhuriyar Nijar ta sanar da katse du wata huldar Diflomatisyya da kasar Ukraine.
Nijar, ta zargi gwamnatin ta Ukraine da goyon bayan kungiyoyin yan ta’adda.
Kakakin gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Amadou Abdramane ne ya bayyana daukar matakin ranar Talata da maraice a wata sanarwa da ya karanto ta gidan talbijin na kasar.
Ya kara da cewa za su shaida wa Majalisar Dinkin Duniya wannan lamari domin ta tattauna kan “kutsen” da Ukraine take yi a yankinsu.
Nijar ta yanke huldar jakadanci da Ukraine ne kwana biyu bayan makwabciyarta Mali ta sanar da daukar irin wannan mataki, sakamakon zargin da ta yi wa mahukuntan birnin Kiev na hannu a hare-haren da ‘yan ta’adda suka kai wa sojojinta inda suka kashe da dama daga cikinsu a kwanakin baya.
Gwamnatin ta sanar a ranar Lahadi, cewa ta lura da wani furuci da ya raina ikon mulkinta da kakakin hukumar leken asiri ta sojojin kasar Ukraine Andrii Yusov ya yi a baya bayan nan, wanda ke tabbatar da hannun Ukraine cikin wani harin wasu kungiyoyi ‘yan ta’adda, da ya rutsa da mutane tare da lalata dukiyoyi ga sojojin Mali, a yakin da suke a arewa maso gabashin kasar.
Sanarwar ta bayyana matakin hukumomin Ukraine a matsayin wanda ya take ‘yancin kan Mali, ya kuma zarce lamarin da kasa da kasa za su iya shiga tsakani, haka kuma takala ce a bayyane ga kasar.