Netanyahu : Biden Ya Tafka Kuskure Wajen Dakatar Da Bai Wa Isra’ila Makamai

Jami’an Isra’ila na ci gaba da raddi wa shugaban kasar Amurka Joe Biden wanda ya yi gargadin cewa Amurka ba za ta samar da makaman

Jami’an Isra’ila na ci gaba da raddi wa shugaban kasar Amurka Joe Biden wanda ya yi gargadin cewa Amurka ba za ta samar da makaman da Isra’ila za ta kai a gagarumin farmaki a kudancin Gaza da ke birnin Rafah, inda dubban daruruwan Falasdinawa ke gudun hijira.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada a wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin a ranar Alhamis cewa Isra’ila, za tayi “yakin ne ko da farce” idan ya cancanta.

Amurka ta ci gaba da baiwa Isra’ila goyon bayan soji a duk tsawon yakin da take yi a zirin Gaza, inda ta bijirewa matsin lamba na kasa da kasa da na cikin gida da kuma kawar da damuwar da ake zargin sojojin Isra’ila na keta dokokin kasa da kasa.

Biden, a wata hira da CNN a ranar Laraba, ya ce har yanzu Amurka ta jajirce wajen kare Isra’ila kuma za ta samar da makaman roka na Iron Dome da sauran makaman kariya amma, idan sojojin Isra’ila suka mamaye Rafah, “ba za mu samar da makamai da manyan bindigogi ba. ana amfani da su.”

Tun da farko a ranar Laraba, sakataren tsaro Lloyd Austin ya ce Amurka za ta dakatar da jigilar manyan makamai.

Lamarin dai ya fiddo a fili rashin jituwa tsakanin gwamnatin Biden da gwamnatin Netanyahu.

A farkon makon nan ne gwamnatin sahyoniyawan ta soma kai hare-hare a gabashin birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza, wanda ya kunshi sama da falasdinawa miliyan 1 da rabi da suka gujewa farmakin sojojin mamaya a zirin Gaza, bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments