Search
Close this search box.

Nasrallah: Yahudawa Ba Za Su Koma Arewacin Falastinu Ba Har Sai An Kawo Karshen Yaki Kan Gaza

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah a ranar Laraba ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka yi shahada ko kuma suka jikkata sakamakon kazamin

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah a ranar Laraba ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka yi shahada ko kuma suka jikkata sakamakon kazamin harin haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar na’urorin sadarwa, inda  Sayyid Nasrallah ya bayyana lamarin a matsayin “babban aikin ta’addanci, aikin kisan kare dangi da kisan kiyashi,” wanda ya kai matsayin laifin yaki.

Harin wanda ya hada da tayar da dubban nau’rorin sadarwa a cikin kwanaki biyu, makiya sun nemi kashe mutane fiye da 5,000 “a cikin mintuna biyu ba tare da la’akari da hadarin hakan ba,” in ji shi.

Ya kuma yi Allah wadai da halin ko-in-kula da maharan ke nunawa a wuraren farar hula inda da dama daga cikin mutanen da ke dauke da na’urorin suke.

Jagoran na Hizbullah ya jaddada cewa harin ya haifar da shahadar mutane da dama ciki har da mata da yara,” tare da jikkata wasu dubbai.

Sayyed Nasrallah ya bayyana harin a matsayin wani babban harin ta’addanci, sannan ya yi jawabi a karo na biyu da Isra’ila ta kaddamar da hare-haren ta’addanci kan dubban masu amfani da na’urar oba-oba, yana mai bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na biyu na Isra’ila na kashe dubban mutane. Ya kuma nuna jin dadinsa kan kokarin da jama’a suka yi na taimakawa da nuna jarunta a lokacin faruwar lamarin.

“Mun kafa kwamitocin bincike kuma muna yin nazari sosai a kan dukkan abubuwan da za su iya faruwa, hasashe, da kuma yuwuwar faruwar haka,” in ji Sayyed Nasrallah. Ya kara da cewa, binciken zai binciki kowane bangare na harin, tun daga masana’antar da aka kera na’urorin zuwa yadda suka shiga hannun  hannun masu amfani da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments