Iran: Dole Ne Makiya Su Mutunta Yarjejeniyar Da Aka Cimma

Shugaban Iran, Masoud Pazeshkian, ya ce wajibi ne a tabbatar da cewa maƙiya sun mutunta yarjejeniyar da aka cimma. Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin ginshiƙin

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Dole ne su tilasta wa maƙiya bi abin da yarjejeniya ta kunsa

Shugaban kasar Iran Masoud Pazeshkian ya ce ya zama dole a yi ƙoƙarin tilasta wa maƙiya su yi aiki da yarjejeniyar da aka rattaba hannu a kanta.

Shugaban Iran ya jaddada cewa ya zama dole a yi ƙoƙarin tilasta wa maƙiya su yi aiki da abin da aka cimma a karkashin yarjejeniyar da aka kulla, yana mai bayyana cewa yarjejeniyar da aka sanya wa hannu ta samo asali ne daga hikimar membobin Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, kuma dukkan mambobi sun amince da ita.

Shugaba Pazeshkian ya rubuta a asusun dandalin sada zumunta na X cewa: “Yarjejeniyar da aka sanya wa hannu ta samo asali ne daga hikimar membobin Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, kuma kowa ya yarda da ita.” Yana ganin wannan yarjejeniya za ta zama cibiyar dangantakarsu ta ƙasashen waje a nan gaba. Dole ne a yi ƙoƙarin tilasta wa maƙiya su yi abin da ya dace. Za a inganta tsaron ƙasar da yankin da kuma abokan hulɗar Iran  saboda wannan yarjejeniyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted