Aragchi Ya Tattauna Da Wasu Kasashen Yankin Dangane Da Tsaro

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ci gaba da tattaunawa da tokwarorinsa a yankin yammacin Asiya dangane da matsalolin tsaro a yankin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana cewa a cikin sa’o’i 24 da suka gabata ya tattauna ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen na kasashen Saudiya, […]

Pezeshkiyan: Dole Ne Bangaren Amurka Ya Kiyaye Alkawali, Kafin Duk  Wata tattaunawa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa takardan fahintar juna tsakanin Iran da Amurka, ita ce abin dogaro ga dukkan hulda da kasashen waje nan gaba, saboda majalisar koli ta tsaron kasar Iran ce ta amince da fahintar junan da ke cikin takardan. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban yana […]

Najeriya Ta Tura Sojoji 86 Da Zasu Yi Aiki Karkashin ECOWAS A Kasar Guinea Bissau

Rundunar Sojin Najeriya ta tura sojoji 86 da za su yi aiki karkashin inuwar rundunar zaman Lafiya ta ECOWAS a Guinea-Bissau,wanda hakan ke kara karfafa hadakar Najeriya da sauren kasashen karkashin inuwar ECOWAS  a batutuwan da suka jibanci zaman lafiya da tsaro a yankin. A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafukanta na sada […]

Kasar Ghana Ta Kaddamar Da Sashen Tace Danyen Mai Don Habbaka Tattalin Arzikinta

Shugaban Ghana John Dramani Mahama, ya kaddamar da sashen tace danyen mai da aka gyara a matatar mai ta Tema, matakin da ya kawo karshen tsaikon aiki da matatar ta fuskanta na tsawon lokaci saboda matsalolin kuɗi da na kayayyakin aiki. A karon farko, matatar ta samu nasarar karɓa da kuma sarrafa gangar mai miliyan […]

Iran: Dole Ne Makiya Su Mutunta Yarjejeniyar Da Aka Cimma

Shugaban Iran, Masoud Pazeshkian, ya ce wajibi ne a tabbatar da cewa maƙiya sun mutunta yarjejeniyar da aka cimma. Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin ginshiƙin dangantakar Iran da ƙasashen waje da kuma ƙarfafa tsaron yankin.

Tattaunawa Tsakanin Iran Da Oman Tana Matakin Karshe

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya ce tattaunawar da ke tsakanin Iran da Oman ta kai mataki na ƙarshe. Ya bayyana cewa bangarorin biyu na tattauna sabuwar hanyar sadarwar teku tsakanin Tekun Farisa da Tekun Oman.

Iran Zata Mayar Da Martani Kan Masu Hada Kai Da Makiya

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya gargadi cewa duk wata ƙasa a yankin da ta haɗa kai da Amurka ko Isra’ila wajen kai hari kan Iran za ta fuskanci martani mai ƙarfi. Ya ce Tehran a shirye take ta kare ikonta da tsaron ƙasa.

Iran Ta Fara Juyayin Shahadar Isma’il Haniyeh

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi bikin tunawa da cika shekaru biyu da shahadar Isma’il Haniyeh, tare da jaddada ci gaba da goyon bayan Falasdinu da kuma kiran a gurfanar da waɗanda ke da alhakin laifukan da aka aikata a Gaza da Yammacin Kogin Jordan.

Ibn Reza: Iran Ba Zata Kai Harin Bazata Ba

Mukaddashin Ministan Tsaron Iran, Majid Ibn Reza, ya ce Iran ba za ta fara kai harin bazata ba, amma ba za ta yi sakaci har a shammace ta ba. Ya jaddada cewa Tehran na ɗaukar kowace barazana da muhimmanci.