Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin hana duk wani tafiye-tafiyen da ministoci da sauran jami’an gwamnati ke yi zuwa kasashen waje. Kuma ya bada umarnin ne ta wata wasika da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Femi Gbajabiamila, ya aike wa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.
Haka zalika , shugaba Tinubu ya bayyana damuwarsa kan dinbin kudaden da ake kashewa wajen wadannan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da jami’an gwamnati ke yi a cikin wannan mawuyacin hali na kokari da ake yi na ceto tattalin arzikin Najeriya da yake tangal-tangal.
Idan ba a manta ba shugaba Tinubu ya bada irin wannan umarni tun abaya ne bayan dandazon jami’an gwamnati sama da 400 suka tafi taron COP28 a Dubai, lamarin da ya jawo cecekuce akai ganin halin matsi da yan najeriay ke fama da tun bayan cire tallafin mai da gwamnatin ta yi.