MDD Ta Gudanar Da Bikin Nuruz Ta Kasa Da Kasa

An gudanar da bukukuwan ranar Nuruz, ko ranar farko ta hijira shamsiyya ta Iraniyawa da kasashe makobta a Majalisar dinkin duniya a jiya Laraba a daya daga cikin zaurukan majalisar a birnin NewYork cibiyar MDD a Amurka. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa bikin Nuruz na bana wato shekara ta 1403 […]
MDD: Yunwa Da Cuttuka Ne Zasu Fi Kashe Mutanen Gaza Nan Gaba

Kwamishinan hukumar UNRWA mai kula da al-amuran bada agaji a kasar Falasdinu da aka mamaye, ya bayyana cewa nan gaba kadin yunwa da kuma cututtuka ne zasu fi kissan falasdinawa a Gaza fiye da makaman HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Philippe Lazzarini, babban jami’i mai kula da hukumar UNRWA yana […]
Masu Zanga-zangar Adawa da Yaki Sun Rufe Manyan Tituna A Birnin Tel Aviv Na Isra’ila

Dubban masu zanga zanga da siyasar yaki da gwamnatin Binyamin na tanyaho ke yi ne suka rufe manya tituna a birnin Telaviv domin nuna rashin amincewarsu da ci gaba da yaki da take yi a yankin gaza bayan da ta kasa kubutar da yahudanwa da da kungiyar Hamas take rike da su. Wannan zanga zangar […]
Dakarun Gwagwarmaya A Kasar Iraki Sun Kai Hari Kan Cibiyar Samar Da Wutar Lantarki Ta Isra’ila

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun gwagwarmaya a kasar Iraqi sun kaddamar da wani sabon hari kan Isra’ila inda suka samu wata cibiyar samar da wutar lantarki a birnin Telaviv a ci gaba da mayar da martani da suka yin a hare-hare da kisan gillan da HKI ke yi wa Falasdinawa, A wata sanarwa da gamayyar […]
Amurka Ta Gabatar Da Babbin Takunkumi Kan Kasar Iran A Kan Kera Makami Mai Linzami

Ma’aikatar Baitil Malin Amurka ta sanar cewa ofishin dake kula da kadarorin gwamnatin tana shirin kakakaba sabbin takunkumi kan wasu cibiyoyi dake Iran turkiya Oman da kuma jamus saboda da zarginsu da taimakawa kasar Iran wajen kera makami mai linzami na Balastic da shirin tan a nakiliya da kuma sauran tsare-tsaren da suka shafi tsaro. […]
Najeriya Ta Soke Duk Wani Tafiye -Tafiyen Da Ministoci Da Mukarraban gwamnati ke yi zuwa kasashen waje

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin hana duk wani tafiye-tafiyen da ministoci da sauran jami’an gwamnati ke yi zuwa kasashen waje. Kuma ya bada umarnin ne ta wata wasika da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Femi Gbajabiamila, ya aike wa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume. Haka zalika , shugaba Tinubu ya bayyana damuwarsa kan […]
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Eidin Noruz Ga Kasashe Makwabta

Amir Abdallahiyan ministan harkokin wajen kasa iran ya aikeda sakonni mabanbanta ga takwararonsa na kasashen Azarbaikan, Uzbakistan ,Afghanistan, Pakistan, Tajikisan,Turkmenistan Turkiya, Iraki, Krygystan ,Kazakhstan da kuma Indiya na murnar shiga sabuwar shekara hijira shamsiya da bikin Eidin Norooz. A jiya laraba 20ga watan maris ne aka fara bukukuwan shiga sabuwar shekara wato shekara ta 1403 […]
Iran: Jagora Ya Ce, Kawancin Masu Gwagwarmaya A Asia Ta Kudu Sun Wargaza Shirin Amurka A Yankin

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae ya yabawa dakaru a cikin kawancen masu gwagwarmaya a yankin Asia ta kudu wadanda suka hada da Gaza Lebanon Yemen da Iraki kan wargaza manufofin Amurka da HKI a yankin Asia ta kudu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto […]
Gaza: Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Ta Bada Sanarwan Cewa Sojojin HKI Sun Kai Hare Hare Fiye Da 400 Kan Asbitoci A Gaza

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bada sanarwan cewa sojojin HKI sun kai hare hare kan asbitoci da cibiyoyin kiwon lafiya fiye da 400 a Gaza tun bayan fara yakin Tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban da ya gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Margaret Harris mai magana da yawun […]