Gwamnatin Nijeriya na kara kokarin bunkasa bangaren ma’adinai ta hanyar jawo masu zuba jari, da fasaha da kwarewa daga kasar Turkiyya domin bunkasa albarkatun ma’adinai. Wannan na zuwa ne bayan kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwuiwa a fannin ma’adinai.
Ministan Raya Ma’adinai na kasa, Dr. Dele Alake, ya ce yarjejeniyar za ta taimaka wajen fadada bincike da sarrafa ma’adinai a Nijeriya, inda ya bayyana cewa duk da an yi bincike ne a kasa da kashi 5 cikin 100 na fadin kasar, amma an gano sama da nau’in ma’adinai masu muhimmanci 44 da suka hada da lithium, da cobalt, da nickel, da tin da sauransu.
Alake ya ce daga cikin muhimman abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa akwai musayar fasaha, da horas da kwararru, da jawo jarin kasashen waje da kuma kare muhalli. Ya jaddada cewa Nijeriya ba ta son ci gaba da fitar da danyen ma’adinai kawai, sai dai tana son a sarrafa su a cikin gida domin kara darajarsu da kudaden shiga.
Ministan ya kuma yi kira ga masu zuba jari na Turkiyya su yi anfani da sabbin sauye-sauyen da gwamnati ta aiwatar a bangaren ma’adinai, ciki har da tsarin lasisi na zamani ta yanar gizo.