Yayan kungiyar yan ta’adda ta ‘the Islamic State West African Province (ISWAP) ta bada sanarwan kamawa da tsare yan mata 13 a karamar hukumar Askira-Uba na jihar Borno a jiya Lahadi.
Jaridar Daily Trust ta Nageriya ta nakalto Abdullahi Askira dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltan Askira yana tabbatar da labarin ya kuma kara da cewa ISWAP ta kama wadan nan yan mata wadanda suke da shekaru tsakanin 13-19 ne a lokacinda suke aiki a gonakinsu a gundumar Mussa na karamar Hukumar ta Askira.
Jaridar ta kara da cewa wannan satar yan mata da yan makaranta ya biyo bayan irinsu da suka yi a makarantar mata ta Maga a karamar hukumar Wasagu na jihar Kebbi da kuma na makarantar St. Marry ta Papiri a karamar hukumar Agwara na jihar Naija duk a arewacin tarayyar Najeriya.
Tun lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump na kasar Amurka yayi barazanar daukar matakin soje a kan Najeriya idan har ta ki daukar mataki kan abinda ya kira kissan kiristoci a kasar ba, kungiyoyin yan ta’adda a arewacin kasar suka kara kaimi wajen satar yan makaranta a arewacin kasar don halattawa Trump gurinsa na mamayar tarayyar Najeriya.