Gwamnati ba zata amince da kiraye kirayen juyin mulki ko kuma daga tutar wata kasa ba.
Jaridar Premium times ta nakalto hafsan tsaron kasa Christoper Musa yana fadar haka a jiya Litinin bayan ganawar jami’an tsaron kasar da shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa a Abuja.
Musa ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa sun tattauna da shugaba Tinubu dangane da kiraye kiraye zuwa juyin mulki, da kuma daga Tutar kasar Rasha wanda wasu masu zanga zanga suka yi a Kaduna na kuma Kano.
Ya ce jami’an tsaron Najeriya gaba daya suna goyon bayan tsarin Democradiyar da ke tafiyar da kasar, kuma zasu yi iya kokarinsu wajen kare tsarin.
Tun ranar daya ga watan Augustan da muke ciki ne aka fara zanga zangar tsadar rayuwa a duk fadin Najeriya, inda a wasu jihohin abin ya zama tashin hankali har saida gwamnatocin jihohin suka kafa dokat hana fita.
Kuma wasu kafafen yada labarai sun ce mutanen akalla 13 suka rasa rayukansu a zanga zangar. Sannan jami’an tsaro sun kama mutane akalla 600 a duk fadin kasar. An shirya gudanar da zanga zangar ne har na tsawon kwanaki 10. A jiya litinin 5 ga watan Augusta dai masu zanga zangar sun fito a birnin Lagos da kuma wasu wurare a arewacin kasar.