Rahotanni daga Najeriya na cewa akalla dalibai 16 ne suka rasa rayukansu biyo bayan ruftawar wani ginin makaranta mai hawa biyu a birnin Jos na jihar Filato da ke tsakiyar kasar.
Rahotonni sun ce lamarin ya farau ne yau da safe kuma dalibai masu yawa ne suka jikkata, yayin da daliban da malamai suka makale a cikin ginin.
Ginin na makarantar Saint Academy – da ke unguwar Busa-buji a karamar hukumar Jos ta Arewa – ya rufta ne a lokacin da daliban ke daukar darussa.
Kawo yanzu dai ba a san dalilin da ya haddasa ruftawar ginin ba.