An ceto da mutane fiye da 300 da masu garkuwa da mutane su ka kama a lokuta mabanbanta a arewacin Nigeria.
Shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu ya bayyana ceto da mutanen da cewa shi ne mafi girma da aka yia rana daya.
Daga cikin wadanda aka ceto da akwai mutan 163 da aka kama a Jahar Kwara, sai kuma wasu mutanen 145 da su ma aka kama su a Jahar Niger.
Babu wani cikakken bayani akan yanyoyin da aka bi, aka ceto da mutanen.
Wata daga cikin mutanen da aka ceto Amira Saliu ta bayar da labarin cewa:
“Sun ajiye mu ne a gabar ruwa. A duk lokacin da jirgin sama yake shawagi a samanmu, za su fada mana cewa mu kashe duk wata wuta da mu ka kunna saboda kar a hango mu.”
Haka nan kuma ta ci gaba da cewa:
” A wani lokacin za su ba mu abinci, a wasu lokutan kuma ba su ba mu. Don haka mu da yaranmu muna kwana da yunwa.
Haka nan kuma a cikinmu da akwai marasa lafiya da mata masu ciki da su ka haihu. Sun tambaye mu idan da akwai unguwar zoma a cikinku, sai na fada musu ni kadai ne. Don haka nake taimakawa mata masu juna biyu. Na taimakawa mata sun kai goma su ka haihu ba tare da safar hannu ta aiki ba.”
Shi kuwa gwamnan Jahar Kwara Abdurrahman Abdurrazq ya yi godiya ne ga Allah saboda ceto mutanen, duk da cewa kamun da aka yi musu tun da fari ba abu ne mai dadi ba.