Fira Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya bayyana cewa: Sun yi watsi da shirin Majalisar Zaman Lafiya game da Gaza, kuma ba za a kafa ƙasar Falasɗinu ba
Fira Ministan gwamnatin Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a yau Lahadi cewa: Isra’ila ta yi watsi da shirin batutuwa 15 na Gaza da “Majalisar Zaman Lafiya” ta amince da shi, yana mai tabbatar da cewa ba zasu janye sojojinsu daga yankin Gaza ba kafin a “karɓe makaman kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da gaske”.
Wannan ya zo ne a cikin wani jawabi da Netanyahu ya yi ta talabijin a farkon taron majalisar ministocinsa na mako-mako.
“Isra’ila ta yi watsi da takarda mai dauke da batutuwa 15 da Majalisar Zaman Lafiya ta Gaza ta wallafa” yana mai karawa da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila ba za su janye daga Gaza ba kafin a kwace makaman kungiyar Hamas.”
Ya jaddada cewa kwace makamai ya hada da “dukkan manyan makamai da kanana,” ya kara da cewa batun “kwace makamai na gaske ne, ba wai kawai kwace makamai na alama ba.”
Netanyahu ya jaddada cewa ba za su amince da kafa wata kasar Falasdinu ba a Gaza ko Yammacin Kogin Jordan muddin shi ne Fira Ministan Isra’ila.
Ya nuna cewa yana tattaunawa da Amurkawa game da shirin Majalisar Zaman Lafiya, yana mai lura da cewa Amurka tana da ra’ayoyi kan lamarin, Isra’ila ta yarda da wasu daga cikinsu, kuma ba da yarda da su ba.”