Falasdinawa Da Dama Sun Jikkata Sanadiyyar Harin Sojojin Mamaya

Kungiyar Hamas dai ta yi kira ga masu shiga Tsakani da su yi wa 'yan mamaya matsin lamba domin su yi aiki da abubuwan da
Kai Wa Palasdinawan GAza Gari

Ma’aikatan Agaji a yankin Gaza sun sanar da cewa wasu Falasdinawa sun jikkata bayan da sojojin mamaya su ka kai hari  a yankunan Khan-Yunus da al-Buraij da kuma Bei-Lahiya.

Wannan harin dai ya biyo bayan wasu sa’o’i kadan da Fira ministan Haramtacciyar Kasar ta Yahudawa da kotun duniya ta manyan laifuka take nema, ya bayyana kin amincewa da wasu bangarori na yarjejeniyar tsagaiwa wutar yaki.

Falasdinawan sun bayyana damuwarsu akan yiyuwar barkewar wani sbon yaki bayan maganganun na Netanyahu.

A can birnin Washington kuwa, kafar watsa labarun nan ta “Axios ta ce; jami’an Amurka ba su damu ba da maganganun Netanyahu saboda an shiga lokacin yakin neman zabe ne.

Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila dai suna son ganin kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun ajiye makamansu da kawo karshen gwagwarmaya, ba tare da la’akari da hakkokin al’ummar ta Falasdinu ba.

Kungiyar Hamas dai ta yi kira ga masu shiga Tsakani da su yi wa ‘yan mamaya matsin lamba domin su yi aiki da abubuwan da aka cimma matsaya akansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted