Jagoran Juyi Ya Yi Sabbin Nade-nade Na tsaro Da Siyasa

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamnei ya nada Muhammad Baqir Zul-Qadar a matsayin mai ba shi shawara a harkokin siyasa.
Hoton jagora Ayatullah Mujtaba Khamnei

jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Mujtaba al-Hussaini Khamnei ya fitar da hukuncin nada Dr. Muhsin Riza’i a ma tsayin babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran.

Sanarar dake tattare da hukuncin ta kunshi cewa:

                     Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Zuwa Ga Dan’uwa Mai Daraja Dr. Muhsin Riza’i

Bisa la’akari da kwarewar da kuke da ita mai girma, ina sanar da nada ku a matsayin wakilina a majalisar koli ta tsaron kasar,bisa la’akari da cewa kun taka rawa mai daukaka a tsawon shekaru 8 na yakin tsaron kasa mai tsarki.

Abin fata shi ne ku sami cikakkiyar nasa da dacewa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanku.

Haka nan kuma ina mika godiya da Dr. Muhammad Bakri Zul-Qadar bisa kwazon da yake cigaba da nunawa.

Muna kuma rokon Allah madaukakin sarki ku ci gaba da zama ma’abocin jihadi wajen yi wa al’ummar Iran mai kwazo hidima a karkashin kulawar ma’abocin zamani, Allah ya gagauta bayyanarsa.

Sayyid Mujtaba Khamnei

A gefe daya, jagoran juyin musulunci na Iran ya nada  Dr. Zul-Qadar Mai Ba Shi Shawara A Harkokin Siyasa

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamnei ya nada Muhammad Baqir Zul-Qadar a matsayin mai ba shi shawara a harkokin siyasa.

Hukuncin Nadin da jagoran juyin ya yi wa Muhammad Baqir Zul Qadar ya kunshi yabawa  kwarewarsa ta aiki tare kuma da yi masa fatan samun dace da nasara a aikin nashi.

Haka nan kuma ya yi masa fatan samun dace a cikin aikin nashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted