Raguwar Makaman Amurka Ne Ya Hanata Ci Gaba Da Yaki Da Iran

Masalin tarihin da siyasa ya kuma kara da cewa; Amurka ta shiga damuwa matuka akan wannan raguwar da makana nata su ka yi, saboda tsoron
Farfesa Cyrus Schayegh ya bayyana ra'ayinsa akan yakin Amurka akan Iran

 Wani masanin tarihi da siyasar kasa da kasa a birnin Geneva ya bayyana cewa; Koma baya mai matsani na makaman Amurka masu linzami ne ya yi tasiri a cikin matakin da yake dauka dangane da Iran.

Kamfanin dillancin labarum “Mehr” na Iran ya nakalto Cyrus Schayegh yana fadin cewa; Da akwai koma-baya mai yawa da makaman Amurka masu linzami suke fuskanta,haka nan kuma sauran na’urorin tsaro da kariya daga hare-hare.

Masalin tarihin da siyasa ya kuma kara da cewa; Amurka ta shiga damuwa matuka akan wannan raguwar da makana nata su ka yi, saboda tsoron brkewar wani rkici a wani yanki ba yammacin Asiya ba.

Cyrus Schayegh ya kara da cewa; Lissafin da Amurka take yi ya hada da yadda al’amurra za su iya kasancewa a gabashin Asiya,don haka idan wani sabon fadan ya barke da Iran, to hakan za iyi gagarumun tasirin tasiri akan matakin da Amurkan za ta iya zaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted