Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI ba zata sake zama da Amurka a teburin tattaunawa ba, matukar da ci gaba da keta yarjeniyar fahintar juna da aka cimma da ita wato (MoU) na Islamabad.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a wato taro a nan birnin Tehran a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa, wannan duk da cewa akwai sakwannni da suke zuwa daga Washington ta hanyar masu shiga tsakani dangane da hakan.
Ya ce, duk tare da wannan kokarin daga wadannan kasashe, Iran ba zata sake komawa kan teburin tattaunbawa da Amurka ba, sai ta canza halayenta ta kuma koma kan Mou na Islamabad.
A ranar 28 ga watan fabrayru na wannan shekarar ne Amurka da HKI suka farma kasar Iran da yaki ba tare da an takalesu ba, suka kashe jagoran juyin juya halin musulunci tare da wasu manya manyan jami’an tsaron kasar. Sannan a cikin fafatawa na kwanaki 40 iran ta amince da dakatar da budewa juna wuta a ranar 8 ga watan Afrilin shekara 2026. Sannan bayan fahintar juna na Islamabad wato mou Amurka ta sake yin watsi da shi ta sake farwa kasar da yaki na kwanaki 13.