Sabon tsarin albashi na sojojin Najeriya ya karu daga mafi karancin Albashi na naira 187,200 zuwa miliyin 3.25.
Jaridar Daily trust ta najeriya ta bayyana cewa sabon tsarin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan satumban shekara ta 2026, wanda ya samar da karin albashi na sojojin kasar daga kasha 30 zuwa 80% a tsakanin mukamai daban daban na sojojin kasar.
Labarin ya kara da cewa sojoji kimani 250,000 ne zasu amfani da wannan sabon karin albashin, wanda jimillar albashin sojojin zai tashi daga naira biliyon N660 zuwa Naira billion N924, kamar yanda mai bawa shugaban kasa shawara kan al-amuran watsa labarao Bayo Onamuga ya bayyana.
A karkashin sabon Alabashin masu mukaman Kanar zuwa sama sun sami karin kashi 30 %, kuma sun hada da brigadier-generals, major-generals, lieutenant-generals da generals. Sai kuma masu mukamaikasa da Kana sun sami karin kasha 50% sannan daga mukamin Private zuwa staff sergeant kuma sun sami karin kasha 80%.
Amma masana sun bayyana cewa wannan karin yayi kadan idan an kwatanta da wasu idan an kwatanta su da wasu kasashen Afirka wadanda suka hada da Afirka ta kudu, Niger da kuma jumhuriyar Benin wadanda suka sama da na sojojin nigherioa da kasha 200% zuwa 800%.