Araqchi: Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: A halin yanzu Iran ba ta tattaunawa da Amurka, kuma sake buɗe mashigar Hormuz ya dogara ne akan

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: A halin yanzu Iran ba ta tattaunawa da Amurka, kuma sake buɗe mashigar Hormuz ya dogara ne akan wasu sharuɗɗa banda yarjejeniyar fahimtar juna da Oman

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Babu wata tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a halin yanzu, yana mai cewa ana musayar saƙonni ta hanyar masu shiga tsakani, kuma wannan ba a ɗaukarsa a matsayin tattaunawa amma kawai musayar saƙonni ne kawai.

Araqchi ya bayyana cewa: Masu shiga tsakani har yanzu suna ƙoƙarin share fagen sake fara tattaunawa tsakanin Iran da Amurka, yana mai ƙarawa da cewa, daga mahangar Iran, ba za a iya ci gaba da tattaunawa ba sai dai idan an daina keta yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin bangarorin biyu kuma Amurka ta biya diyya na hasarorin da ta janyo wa sakamakon keta yarjejeniyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted