Mutane 13 Sun Mutu Wasu 14 Kuma Sun Jikata A Afghanistan Sakamakon Harin Da Pakistan Ta Kai Mata

Rahotanni sun nuna cewa kimanin 13 ne suka mutu yayin da wasu guda 14 kuma suka jikkata bayanda kasar Pakistan ta kai hari a kasar

Rahotanni sun nuna cewa kimanin 13 ne suka mutu yayin da wasu guda 14 kuma suka jikkata bayanda kasar Pakistan ta kai hari a kasar Afghanistan adaidai lokacin da rikicin kan iyake yaka kara ta’azzara, kuma an kai harin ne a lardin khost da kuna da paktika kamar yadda kakakin gwamatin Taliban zabihullah mujahid ya bayyana.

Jami’an gwamnatin kasar Afghanistan sun bayyana cewa cikin wadanda suka mutu sakamakon harin akwai yara guda 11 sai mace daya da kuma wani tsoho guda daya, sai dai babu wani karin bayani da ya fito daga bangaren Pakistan game da harin.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Pakistan ta bayyana cewa an yi mummunan musayar wuta inda wasu mambobi guda 6 suka mutu yayin da wasu da dama kuma suka jikkata, sai dai wata majiya ta jami’an tsaro daga baya sun kashe mutane 8 daga cikin maharan kuma sun hanasu wucewa ta inda aka sanya shingen shige da fice na ababen hawa.

Ministan cikin gidan sayed muhsin raza Naqvi ya halarci wajen jana’izar wanda aka kashe a peshavar kuma yace Pakistan za ta gudanar da bincike kan masu kai harin dake neman zama barazana da tsaro da zaman lafiyar kasar

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted