Babban kwamandan sojoji kasa JMI ya bayyana cewa shugaban kasa yana da babban rawan da zai taka a wajen tabbatar da tsaron kasa tun da shine shugaban majalisar koli ta tsaronkasa.
Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya nakalto Baban kwamandan sojojin kasa na JMI Sayyid AbdurrahimMusawi yana fadar haka a wata tattaunawa da IRIB NEWS dangane da matsayin shugaban kasa wajen kare kasa da kuma yadda yake mu’ala da sojojin kasa, na kasa.
Janar Musawi ya kara da cewa sajojin kasa a JMI sune a gaba gaba wajen tabbatar da tsaron kan iyaka na kasa da sauran kasashe makobta na kuma na ruwa, amma sauran bangarorin tsaro na kasar suna da rawar da suke takawa a wannan bangaren.
Musawi ya kara da cewa shugaban kasa a matsayinsa na shugaban majalisar koli ta tsaron kasa, wannan matsayin yana da muhimanci kuma yana iya taimaka wajen karfafa tsaron kasa.
Janar musawi ya kamala da cewa duk wanda aka zaba a matsayin shugaban kasa sojojin kasa, na kasar a shirye suke su yi aiki tare da shi don tabbatar da tsaron kasa da kuma karfafa sojojin kasar.