Kafofin yada labaran Morocco da na Isra’ila sun bayyana cewa Rabat na da niyyar sayen tauraron dan adam na leken asiri daga kamfanin masana’antar sararin samaniyar Isra’ila a wani bangare na yarjejeniyar da ta kai dala biliyan daya.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga kamfanin kula da harkokin sararin samaniya na Isra’ila cewa, ya kulla wata yarjejeniya ta dala biliyan daya domin samar da daya daga cikin na’urorinsa ga wani bangare na yarjejeniya da Morocco.
Kamfanin wanda ke kera na’urorin kariya na makamai masu linzami da jirage marasa matuka a Isra’ila, ya bayyana a cikin wata sanarwa ga hukumomin da ke Tel Aviv cewa an tsara aiwatar da yarjejeniyar na tsawon shekaru 5.
Kafofin yada labarai na kasar Morocco “Le Desk” da “Le 360” sun ruwaito cewa, “kwangilar ta tanadi cewa kamfanin zai samar da tauraron dan adam na Ofek-13, wanda zai maye gurbin tauraron dan adam guda biyu da kamfanonin Airbus da Thales suka samar.”
Hakazalika, kafofin yada labaran Isra’ila daban-daban sun bayar da wannan rahoto, daga ciki har da shafin yanar gizon “Calcalist” na Isra’ila, wanda ya ƙware a kan labaran fasaha, ya ruwaito cewa “Moroco za ta sayi tauraron dan adam don ayyukan leken asiri daga masana’antar jiragen sama akan dala biliyan daya.”
Rahotanni sun ce yarjejeniyar sayen tauraron dan adam na leken asiri na Isra’ila tsakanin Isra’ila da Maroko ta fara ne a karshen shekarar 2023.
Kasar Maroko dai na daga cikin kasashen larabawa da suka kulla alaka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila a shekarun baya, duk kuwa da cewa tun kafin nan kasashen biyu suna gudanar da harkokinsu a boye.