Ministan Wajen Kasar Iran Abbas Araqchi Ya Tattauna Da Takwarorinsa Na Yankin Kan Ci Gaban Da Aka Samu

Rahotani sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya  tattaunawa ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen kasashen yakin bayan martanin da

Rahotani sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya  tattaunawa ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen kasashen yakin bayan martanin da kasar iran ta mayar kan HKI sakamakon hare-haren da ta kaddamar a yankin Dahiya na kasar Labanon.

Ministan na iran yace ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Masar Badr abdelatty da kuma na kasar faransa  Jean Noel Barrot da na kasar Iraki Fuad hussain, da na kasar Qatar shaikh mohammad bin Abdurrahamna al- thani da na kasar saudiya faisal bin Farhan da na Turkiyya Hakan fidan da kuma sakatariyar harkokin wajen birtaniya Yvette Cooper da kuma babban kwamandan sojojin kasar Pakistan Asim Munir, kuma sun tattaunawa kan sabbin ci gaban da aka samu a yankin bayan martanin da kasar iran ta kai kan keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da HKI ta yi kan kasar labanon. Haka zalika ya bayyana cewa tun tuni iran tayi gargadin cewa idan hare-haren Isra’ila ya ci gaba zuwa yankin Dahiya to ko shakka babu iran za ta mayar da martani a yankuna daban –daban na Isra’ila, don haka wajibi ne Isra’ila ta dakatar da hare-haren da take kai wa, idan kuma ba haka ba za ta fuskanci mayar da martani mai tsanani da zai sanya ta yi nadama .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted