Ministan tsaron kasar Venezuela Vladmir Lopez ya bayyana cewa; har yanzu Nicholas Maduro ne harlartaccen shugaban kasar, kuma ba su laminta da garkuwa da shi da Amurka ta yi ba da kuma mai dakinsa.
Ministan tsaron kasar ta Venezuela ya kuma kara da cewa; Rundunar kasar ta Venezuela ba ta laminta da sace shugaban kasa Maduro da maidakinsa da Amurka ta yi ba.
Haka nan kuma ya yi Ishara da cewa a yayin harin da Amurkan ta kai wa kasar ta kashe jami’an tsaron da suke bayar da kariya ga shugaban kasar, sannan kuma ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su yi la’akari da hairn na wuce gona da iri akan Venezuela da keta huruminta da Amurkan ta yi.
Sai dai kuma ministan na tsaron kasar ta Venezuela ya bayyana yadda kasashen duniya da al’ummunta suke nuna goyon bayansu ga Venezuela, yana mai bayyana Amurka a matsayin baraza ga tsaron duniya da zaman lafiya.
Haka nan kuma ministan ya bayyana cewa, bisa amincewa da shawarar kotun kolin kasar, tuni an rantsar Delcy Eloína Gómez a matsayin shugabar kasa.
A ranar Asabar da tsakar dare ne Amurka ta kai hari a cikin kasar Venezuela, tare da kamo shugaban kasar Nocholas Maduro da mai dakinsa, ta kai su kasarta.