Ministan harkokin wajen kasar Oman wanda yake shiga tsakanin tattaunawar da ake yi a tsakanin Iran da Amurka ya ce, yana da tabbacin kasashen biyu za su iya cimma matsaya.
Badar Bu Sa’idi wanda tashar talabijin dain CBS ta yi hira da shi, ya bayyana cewa; Idan har mu ka bai wa diplomasiyyar damar ta yi aiki, to za a kai ga cimma matsaya ta zaman lafiya.”
Bu Sa’idi ya kara da cewa; Babu wani zabin wanda ba na diplomasiyya ba wanda zai iya warware matsalar da ake da ita.
Haka nan kuma ya yi Ishara da ci gaban da aka samu a tattaunawar kasashen biyu, sannan kuma ya nuna fatansa na ganin an ci gaba da tafiya akan inda aka tsaya.
Ya kuma ce, a tashi fahimtar muhimmin ci gaban da aka samu shi ne yadda amincewar Iran aka cewa ba za ta mallaki duk wasu sanadarori na kera bomb ba, a nawa tunanin wannan shi ne babban ci gaba.
Har ila yau, Bu Isa’idi ya ce; Idan har manufar tattaunawar ita ce, ganin Iran ba ta kera makaman Nukiliya ba, to a zatona an samu gagarumin ci gaba ta hanyar wannan ttataunawar da ake yi.
Da yake amsa tambaya akan yakin harin wuce gona da iri na shekarar da ta gabata wacce Isra’ila ta kawo wa Iran da kuma yiyuwar sake maimaita shi, Bu Sa’idi ya ce; Ba mu fatan ganin abinda ya faru a shekarar da ta gabata ya sake maimaita kansa, kuma dukkanin duniya tana cikin halin damuwa akan hakan, don haka ina tunanin duniya tana son ganin an cimma yarjejeniya, saboda a fice daga halin da ake ciki.