Araqchi: Namijin kokarin al’ummar Iran abin yabawa ne

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin ‘yan sahayoniyya a yakin kwanaki 12 Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin ‘yan sahayoniyya a yakin kwanaki 12

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin yahudawan sahayoniyya a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa. A lokacin da yake halartar taron manema labarai da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya gudanar a yau Litinin, Araqchi ya ce: Na farko dai ya zama wajibi a gare shi ya girmama dukkanin shahidai: shahidan juyin juya halin Musulunci, shahidan tsaro mai alfarma (1980-1988), da dukkanin shahidan da suka sadaukar da rayuwarsu wajenkare kasa, tun farko-farko har zuwa yau, musamman ‘yan jaridu da shahida yakin matsorata masu wuce gona da iri na yakin kwanaki 12.”

Ministan harkokin wajen kasar ya kara da cewa: Babu shakka wannan yaki zai kasance daya daga cikin abubuwan da ba za a taba mantawa da shi ba a tarihin Iran na yau da kullum, yakin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya masu laifi tare da goyon baya da hadin gwiwar manyan kasashen duniya da sauran su suka kaddamar na wuce gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da fatan cimma munanan manufofinsu da wani harin ba-zata cikin kankanin lokaci, to sai dai al’ummar Iran sun sake tabbatar cewa sun yi tsayin daka tare da zage dantse babu abin da zai kawar da su kan azamarsu, saboda mutane suna ne da saiwoyinsu suka shimfiɗa a cikin kasa sama da dubban shekaru, saiwoyin suke kara karfi kowace rana, ƙasar da ta wanzu saboda sadaukarwa, da tsayin daka, da Imani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments