Ministan Harkokin wajen Kasar Iran Ya Ce Makaman Nukliya Basa cikin Shirin Makamashin Nukliyar Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi ya bayyana cewa kera makaman Nukliya baya daga cikin shirin amfani da fasahar Nukliya na kasar. Kamfanin dillancin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi ya bayyana cewa kera makaman Nukliya baya daga cikin shirin amfani da fasahar Nukliya na kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a jiya talata a lokacinda yake gabatar da Jawabi a taron MDD na kwance damarar makaman nukliya a duniya wanda aka gudanar a birnin Geneva na kasar Swissland.

Ministan ya tabo batutuwa da dama dangane da shirin Iran na makamashin Nukliya, inda ya ambaci rufe idanun da manya manyan kasashen duniya da kuma hukumar IAEA suka yi dangane da shirin HKI na nukliya. Ya ce kowa ya san cewa HKI ta mallaki makaman Nukliya, amma kuma ba wanda zai yi magana a kan wannan, sai shirin makamacin nukliya na kasar Iran wanda babu tabbas kan cewa iran tana da wannan shirin.

Aragchi ya kara da cewa gwamnatin JMI bata da wani shiri ko a boye da mallakar makaman Nukliya, amma tana bukatar amfani da fasahar Nukliya don ayyukan zaman lafiya kuma tuna ta fara samun amfanin hakan.

A wani bangare na jawabinsa ministan ya bayyana cewa Iran ba zata taba amincea ta tattauna da wata kasa kan al-amuran da suka shafi tsaron kasarta ba. Daga cikin har da makamanta masu linzami wadanda suke cin dogon zango ko kuma shirinta na siyasa a gabas ta tsakiya da sauran kasashen duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted