Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Bayani Kan Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da Amurka Take Yi

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi tir da gwamnatin Amurka saboda ci gaba da keta yarjeniyar ranar 8 ga watan Afrilun wannan

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi tir da gwamnatin Amurka saboda ci gaba da keta yarjeniyar ranar 8 ga watan Afrilun wannan shekarar, tare da kai hare hare a kudancinkasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na gwamnatin kasar Iran ya nakalto Abbas Aragchi yana cewa Amurka ta kai hare hare kan na’urorin rada na kasar da ke yankin Sirk da kuma tsibirin Qishm na yenkin tekun farisa a jiya Asabar.

Ya kuma kara da cewa yin haka ya keta dokokin kasa da kasa wadanda suka shafi diyaucin wata kasa mai cikekken yanci.

Yace wannan ci gaba ne da ayyukan ta’addancin da Amurka da HKI suka sha yi a kasar Iran wanda ya nuna rashin mutunta dokokin kasa da kasa wanda gwamnatin kasar Amurka take yi.

A jiya asabar ne wasu jiragen daukar man fetur na kasar Amurka guda 4 suka yi kokarin ficewa daga mashigar ruwa ta hurmus, amma sojojin IRGC suka buge da daga cikinsu suka lalatata, sai sauran kuma suka koma baya.

A nan ne sai Amurka ta kai hari kan na’urorin sadarwa na kasar dake sirin da kuma tsibirin Qishm, a nan ne Iran ta maida martani da makamai masu linzami kan sansanonin Amurka da suke kasashen Bahrain da UAE.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted