Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Isa Birnin Islamabad Na Kasar Pakistan

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya isa birnin Islamabad na kasar Pakitsan domin ganawa da mahukuntan kasar akan halin da ake

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya isa birnin Islamabad na kasar Pakitsan domin ganawa da mahukuntan kasar akan halin da ake ciki a wannan yankin da kuma alakar kasashen biyu.

 Kamfanin dillancin labarun “Irna” na Iran ya nakalto cewa; A yayin da  Abbas Akakci tare da tawagar da take rufa masa baya su ka isa birnin Islamabad, sun sami tarbar mataimakin Fira  ministan kasar Sanata Muhmmad Ishaq Dar, da ministan harkokin cikin gida Muhsin Taqwi, da babban hafsan hafsoshin sojan kasar Field Marshal Sayyid Aism Munir, sai kuma jakadan Iran a kasar ta Pakistan Riza Amiri.

Gabanin tafiyar tashi, ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya wallafa sako a Shafin sada zumunta dake cewa:

” Zan yi tafiya zuwa Islamabad, Mscut da kuma Moscow. Manufar wannan ziyarar ita ce, yin aiki tare da abokanmu akan alakar bangarorin biyu, da kuma tuntubar juna akan halin da ake ciki a wannan yankin. Makwabtanmu sune ke da muhimmanci.”

Babu wani tsari akan cewa tawagar ta Iran za ta gana da tawagar Amurka a yayin wannan ziyarar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted