Ministan harkokin wajen Iran ya fara ziyarar aiki a kasashen Pakistan, Oman da kuma Rasha

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulinci ta Iran, Abass Araghchi, ya fa wani ran gadin aiki a kasashen Pakistan, Oman da kuma Turkiyya. Mista Araghchi ya

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulinci ta Iran, Abass Araghchi, ya fa wani ran gadin aiki a kasashen Pakistan, Oman da kuma Turkiyya.

Mista Araghchi ya isa birnin Islamabad na Pakistan a ranar Juma’a da dare.

Zai tattauna da mahukuntan Pakistan kan batutuwa da dama da suka shafi kasashen, halin da ake ciki a yankin da dai saurensu.

Sabanin yadda wasu kafofin yada labarai suka rawaito Iran ta musanta cewa ziyarar ta Araghchi na da alaka da bukatar da Amurka ta gabatar na Iran ta gaggauta shiga tattaunawa.

Iran ta ce babu wata tattaunawa ta kai tsaye da aka tsara yi tsakanin tawagar Washington da Tehran.

Babban makasudin ziyarar shi ne tattaunawa da abokan huldarmu kan batutuwan da suka shafe mu da kuma tuntuba kan halin da ake ciki a yankin inji Abass Araghchi a shafinsa na ”X” gabanin ya tashi daga Tehran zuwa Islamabad.

Wanan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa tawagar Amurka na shirin zuwa Pakistan domin tattaunawa da Iran.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted