Ministan harkokin wajen kasar Iraki “Fu’ad Hussain ya iso Tehran a wata ziyarar aiki da zai gana da mahukuntan kasar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ce; A yayin wannan zaiyarar za a yi ganawa a tsakanin ministan na Iraki da takwaransa na Iran, da kuma manyan jami’an gwamnatin kasar.
Daga cikin wadanda zai gana da su da akwai shugaban kasa Mas’ud Pizishkiyan da kuma shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Qalibf. Haka nan kuma manyan jami’an tsaro na kasar Iran.