Hukumar samar da abinci ta MDD ta bukaci a bude duk wasu hanyoyi domin shigar da abinci a Zirin Gaza, saboda yadda magance matsalar yunwa a Zirin zai dauki lokaci.
Kakakin WFP Abeer Etefa ta shaidawa manema labarai a Geneva cewa, za a dauki lokaci kafin a rage yunwa.
“Yanayi a Gaza yana da matukar wahala kuma har yanzu muna da nisa daga cimma wannan burin,” in ji ta.
A cewar WFP, bukatar gaggawa ta ta’allaka ne ga “bude mashigar kan iyaka guda biyar” zuwa cikin yankin “domin a wadata Gaza da abinci da kuma samar da wuraren rarrabawa cikin gaggawa,”.
Shirin WFP, “shi ne kara yawan taimakon da za a kai ga mutane miliyan 1.6 a cikin Gaza cikin watanni uku masu zuwa,” in ji Madam Etefa
A ranar Alhamis din da ta gabata ministan harkokin wajen Isra’ila Gideon Sa’ar ya sanar da cewa wata kila a bude mashigar Rafah tsakanin zirin Gaza da Masar ranar Lahadi.
Majalisar Dinkin Duniya da manyan kungiyoyi masu zaman kansu na yin kira da a bude wannan mashigar, yayin da zirin Gaza ke fuskantar mummunar matsalar jin kai sama da shekaru biyu na yakin da aka fara a watan Oktoban shekarar 2023.
A cikin watan Agusta, kwararrun abokan hulda na Majalisar Dinkin Duniya sun tabbatar a hukumance cewa ana fama da yunwa a zirin Gaza.