MDD Ta Yi Maraba Da Cimma Yarjejeniyar Yin Zabe A Kasar Libya

 Kwamitin tsaro na MDD ya yaba wa yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin kungiyoyin siyasa da suke rikici da juna, domin tsara zabuka a cikin

MDD

 Kwamitin tsaro na MDD ya yaba wa yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin kungiyoyin siyasa da suke rikici da juna, domin tsara zabuka a cikin shekaru biyu masu zuwa.

MDD ta taimaka wajen cimma wannan yarjejeniyar a tsakanin bangarorin siyasar kasar amsu adawa da juna wacce aka rattaba hannu akanta a ranar 30 ga watan Ogusta.

Waikilin kasar Faransa a kwamitin tsaron MDD Jerome Bonnafont wanda kuma kasarsa ce take jagorantar kwamitin, ya bayyana cimma wannan yarjejeniyar da cewa mataki  ne mai muhimmanci da zai kai ga yin zabe mai inganci.

Kwamitin tsaron na MDD ya kuma bayyana cewa; Dukkanin bangarorin siyasar kasar Libya sun nuna goyon bayansu ga wannan yarjejeniyar,tare kuma da karfafa musu gwiwa da su tabbatar da an cimma gaci.

Tun bayan da kasashen turai da da Nato da kuma hadin bakin wasu kasashen larabawa su ka kifar da gwamnatin Mu’ammar Khaddafi a 2011,kasar ta Libya ta fada cikin rikici da rashin tsayayyar gwamnati guda daya mai karfi.

Da akwai gwamnatoci biyu a kasar Libya a gabashi da kuma yammaci da ba su ga maciji da juna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted