Sojojin Isra’ila Sun Kashe Wani Bafalasdine A Yankin Gaza

sojojin isra'ila sun kai hare are a gabar yammacin kogin jodan kuma sun kashe wani ba falasdine kuma sun saje gawarsa

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Isra’ila sun kashe wani bafalasdinu  dan  shekaru 29 da haihuwa a wani hari da suka kai a garin aqraba dake gabar yammacin Jodan inda suka kai hari kan gidansa kuma suka yi amfani da nakiya akan gidan kafin su rusa wani bangarensa.

Ma’aikatar lafiya ta yanki gaza ta bayyana cewa bafalasdine da aka kashe sunansa Abdul karim mohammad salem khader kuma sojojin Isra’ila ne suka harbe shi  kafin daga baya su kashe shi a garin aqraba dake kudancin Nablus a yankin na gaza a ranar talata da ta gabata

kamar yadda yazo a cikin rahoton sojojin isra’ila sun kai samame a garin Aqraba inda suka kewaye gidan Khader suka yi amfani da nakiya wajen tarwatsa gidan kafin daga baya su sanya motar buldoza wajen rushe wani bangare gidan harin ya lalata gidan inda yayi manyan lamuka.

kakakin sojin Isra’ila  yayi ikirarin cewa sun kashe wani mutum da yayi kokarin kai ma sojojinsu hari, sai dai shugaban garin na Aqraba salah addin jaber ya bayyana cewa Khader bashi da makami a hanunsa shi yasa ma bayi musayar wuta ba, kuma kimani sojoji 300 zuwa 400 ne suka kutsa kai a ckin garin cikin dare kuma suka killace gidansa tare da bayyana shi a matsayin yankin soji, inda suka kashe shi kuma suka tafi da gawarsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted