Kasar iran tayi watsi da kudurin da hukumar kula da makamashin nukiliya ta zartar wanda ya tura batun shirin iran ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, kuma tayi gargadin cewa matakin siyasa da aka dauka zai kara taimakwa sosai wajen lalata tsarin hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, kuma yana watsi da gaskiyar yakin da ake ci gaba da yi
Wannnn bayani ya zo ne a jiya laraba bayan fitar da wani kuduri da kasar Amurka, birtaniya, faransa da kasar Jamus suka gabatar da ya samu ra’ayi 23 da suka amince da shi a kuri’ar da aka kada, inda kasashe uku suka nuna rashin amincewa da shi wato kasashen Rasha Niger da kuma kasar China yayin da wasu kasashen guda 8 kuma sun kauracema kada kuri’a
Kudurin ya bukaci darekta janar na hukumar kula da makamashin nukiliya na duniya Rafael Grossi da ya gabatar da iran gaban kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya wanda shi ne karon farko a cikin shekaru 20 da aka mika batun iran din ga kwamitin game shirinta na nukiliya na zaman lafiya,
A cikin wani bayani da jakadan iran a hukumar dake viyanne ya wallafa a shafinsa na X ya yi suka mai tsanani game da amincewa da kudurin yana mai cewa lallai tsarin hana yaduwar makaman nukiliya ya kama hanyar rushewa baki daya, kuma iran ta dora alhakin rikicin nukiliyar na yanzu kan Amurka da isra’ila kan yakin da suka tayi da kasar iran