Dan Majalisar Amurka : Gwamnatin Trump Ce Mafi Muni A Tarihi

wani dan jamiyar demukorat a Amurka yace gwamnatin trump ce mafi muni a tarihi

Robet Gasiya mamba a jam’iyar demukurat kuma dan majalisar dokokin kasar Amurka daga yankin kalfoniya acikin wani bayani da yayi na sukar siyasa da mataken da shugaban Amurka Donald trump yake dauka ya jaddada cewa gwamnatin Trump itace mafi munin gwamnatin da aka taba samu a tarihin kasar Amurka

Haka zalika kasiyo da yake tattaunawa da manema labarai ya bayyana cewa muna so mu samu natsuwar cewa shin alummar Amurka za su iya rayuwa cikin walwala, su gudanar da ayyukansu kuma su samu kulawa da lafiyarsu, amma shugaban kasa ya shagaltu da yada sakonni masu ban mamaki da takaici, da tada hankali a kafafan sada zumunta na zamani, yace ya zama wajibi mu bayyana, wannan it ace gwamnati mafi muni.

Dan majisar ya ci gaba da cewa adaidai lokacin da Trump da iyalansa suke kara zama hamshaken masu kudi sosai, su kuma sauran alummar Amurka sai kara rauni suke yi , kuma da kyar suke iya samar da kudaden da zasu kula da rayuwarsu

Yan Demukurat a Amurka sun sanar da wani babban shiri na binciken Donald trump da iyalansa da kuma  gwamnatinsa, wani bincike da suka ce zai fi mayar da hankali ne kan zarge zargen cin hanci da rashawa da kuma muradun kudi na kashin kai da kuma yiyuwar amfani da ikon shugaban kasa ba bisa kaida ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted