An fitar da jerin sunayen ‘yan wasan da aka zaba don neman kyautar gwatzon ɗan wasa na Ballon d’Or ta shekarar 2026, wanda ke nuna cika shekaru 70 da fara bayar da wannan kyauta domin karramawa da kuma bikin murnar manyan nasarori a duniyar kwallon kafa a kakar wasa ta 2025/26.
An sanar da sunayen wadanda aka zaba din ne ta shafin hukumar bayar da kyautar a dandalin X a ranar Talata.
Har ila yau, an sanar da sunayen wadanda aka zaba a wasu bangarorin, kamar su gwarzon dan wasan gaba (na maza da mata), matashin ɗan wasa mai hazaka ta musamman, masu tsaron gida, kungiyoyi, da kuma masu horarwa da suka yi fice a kakar wasan da ta gabata.
Sannan ɗan wasan gaba na Barcelona, Lamine Yamal, ya kafa tarihi a ranar Talata ta hanyar zama dan wasa na farko da aka zaba don neman kyautar Ballon d’Or sau uku kafin ya cika shekaru 20 a duniya.
Matashin mai shekaru 19 ya zo na biyu a bara, inda ya zo bayan Ousmane Dembele na kungiyar ƙwallon ƙafar PSG a sakamakon karshe na kyautar Ballon d’Or.
Yamal ya zura kwallaye 24 tare da bayar da kwallayen da aka ci guda 15 a wasanni 45 da ya taka leda a gasanni daban-daban tare da Barcelona, sannan ya kuma taka muhimmiyar rawa a tawagar Hansi Flick yayin da suka yi nasarar kare kambunsu na gasar La Liga da kuma Supercopa de Espana.